Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Gasar Kofin Nahiyar Afirka Ta AFCON


Kofin gasar AFCON (AP)
Kofin gasar AFCON (AP)

Najeriya na rukunin 'A,' mai dauke da Ivory Coast, Guinea-Bissau da kuma Equatorial Guinea.

An fara gasar kofin nahiyar Afirka ta AFCON a ranar Asabar a Abidjan babban birnin Ivory Coast.

Daga cikin zakarun ‘yan wasan nahiyar da ke kokarin lashe kofin akwai Victor Osimhen na Najeriya, wanda shi ne ya lashe kambun zakaran dan wasa a nahiyar a bara.

Akwai kuma Mohamad Salah na kasar Masar da suka fafata da Sadio Mane na Senegal da ta lashe kofin.

Gasar na wakana ne a karo na 34.

Senegal za ta yi kokarin kare kofin wanda ta lashe a shekarar 2022 a Kamaru yayin da kasashe irinsu Najeriya, Morocco da Masar suka yunkuro don su raba ta da kofin.

Wannan shi ne karo na farko cikin shekaru 40 da kasar Ivory Coast za ta karbi bakuncin wasan.

Kasashe 24 ne za su fafata a wannan gasa wacce za a kammala a ranar 11 ga watan Fabrairu.

Wasa na farko an kara ne tsakanin Ivory Coast mai masaukin baki da Guinea-Bissau a filin wasa na Alassane Ouattara da ke Ebimpe mai daukan mutum dubu 60.

Najeriya na rukunin A, mai dauke da Ivory Coast, Guinea-Bissau da kuma Equatorial Guinea.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG