Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zan Mika Mulki Ranar 28 Ga Watan Mayu- Jonathan


Shugaban Najeriya mai barin gado, Goodluck Jonathan
Shugaban Najeriya mai barin gado, Goodluck Jonathan

Yayin da rage makwanni kadan jam'iya mai mulki ta PDP ta mika ragamar mulkin kasar ga zababbiyar gwamnatin APC, Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya ce ya yanke shawarar mika mulki a ranar 28 ga watan Mayu maimakon ranar 29.

Shugaban Najeriya mai barin gado, Goodluck Jonathan ya ce ranar 28 zai mika mulki ga gwamnatin zababben shugaban kasa Muhammadu Buhari, kwana guda kafin a rantsar da sabuwar gwamnatin.

Ministar yada labarai, Patricia Akwashiki, ta ce shugaban Jonathan ya bayyana hakan ne a taron masu gudanar da ayyukan gwamnati da aka yi jiya laraba.

“Ranar 28, shugaban kasa ya tsaida cewa zai mika mulki domin a bar ranar 29 a matsayin rabar da za a rantsar da sabuwar gwamnati.” In ji Akwashiki.

Ministan ta kuma kara da cewa ana sa ran za a kammala komai tare da yiwa gwamnati mai shigowa maraba.

Zababben shugaban kasa Muhammadu Buhari ya lashe zaben kasar ne wanda aka yi a ranar 28 ga watan Maris a karkashin jam’iyar APC wanda hakan ya kawo karshen mulkin PDP da ta kwashe shekaru 16 ta na mulkar kasar.

XS
SM
MD
LG