Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Bincike Kan Mata 14 Da Suka Kamu Da Cutar Zika a Amurka


A jiya ne cibiyar ta CDC da ke jihar Atlanta ta yi sanarwar

Cibiyar kula da magance cututtuka ta Amurka da ake kira CDC ta ce ta na binciken wasu rahotanni da suka nuna cewa wasu mutane su 14 da su ka kamu da cutar Zika a Amurka, ana zaton ta hanyar juma’i su ka kamu da cutar.

A jiya ne cibiyar ta CDC da ke jihar Atlanta ta yi sanarwar ta kuma ce duk wadanda suka kamu da cutar mata ne wanda kuma hanya daya ce za iya cewa sun kamu da cutar, wato saduwa da namijin da ya ziyarci inda ke fama da cutar kwanan nan.

Cibiyar na kira ga maza da suka je yankunan da ke fama da cutar kwanan nan su yi amfani da kwararon roba ko kuma ma su kauracewa yin juma’I da mata masu juna biyu ko kuma wadan da ke da niyyar ko fatan samun juna biyu.

Duk da cewa ana kamuwa da cutar ta hanyar juma’ai, jami’an kiwon lafiya sun ce har yanzu cizon sauro ne babbar hanyar yada cutar, kuma cibiyar na kira ga jama’a da su yi amfani da gidajen sauro da magungunan kiyaye cizon sauro ko sanya dogayen kaya.

XS
SM
MD
LG