Fatar mutanen Najeriya da Jamhuriyar Nijar ta samun sauki bayan samun nasarar bude iyakokin kasashen biyu na fauskantar cikas saboda kawo yanzu ba a samu wani sauyi na azo a gani ba ni duk da yake Najeriya ta bude iyakokin ta tun makon jiya.
A ci gaba da kwan gaba kwan baya da huldar Jamhuriyar Nijar da wasu kasashen Yamma ke yi, kasar da ke karkashin mulkin soji, ta yi shelar yanke huldar soji da Amurka.
Kungiyar agaji ta SOS Mediterranee a yau Alhamis ta ce, wasu da aka ceto daga wani jirgin ruwan roba da ya barke a tsakiyar tekun Mediterrenean, sun sanar da cewa, wasu mutane 50 da suka tashi daga kasar Libya tare da su mako guda da ya wuce sun halaka a cikin wannan tafiya.
Wata tawagar manyan jami’an gwamnatin Amurka da ke ziyara a jamhuriyar Nijar na ci gaba da tattaunawa da hukumomin rikon kwayar kasar a wuni na uku domin jin inda aka kwana game da tsare-tsaren jadawalin gudanar da al’amuran mulkin rikon kwarya.
‘Yan sandan kasar Zimbabwe a ranar Larabar da ta gabata sun ce sun kama wani mutum da ke da’awar cewa shi Annabin mabiya darikar manzanni ne a wani wurin ibada da mabiyansa ke zama a wani waje.
Ministar harkokin wajen Afirka ta Kudu ta ce za su kama 'yan kasar da ke yaki da sojojin Isra'ila ko kuma tare da su a Gaza idan sun komo gida.
Najeriya ta samo tallafin dala biliyan 1.3 domin kammala aikin layin dogo da zai hada Kano, birni mafi girma a arewacin Najeriya zuwa Maradi dake makwabciyar kasar Nijar, in ji ma'aikatar sufuri a ranar Laraba.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bada umarnin gaggauta bude kan iyakokin Najeriya da Jamhuriyar Nijar. Haka kuma, ya umarci a janye dukkanin takunkuman da aka kakabawa kasar nan take.
Wata kotu a Uganda a ranar Talata ta yi watsi da bukatar da wata kungiya mai fafutukar kare hakkin bil adama ta LGBT ta shigar da ke neman tilasta wa gwamnati yin rajista, in ji lauyan mai shigar da kara.
Aljeriya na shigo da naman sa da na rago mai tarin yawa domin tunkarar yanayi bukatu na naman da ake sa ran amfani da shi a duk watan Ramadan mai alfarma, tare da fatan daidaita farashin yayin da tattalin arzikin kasar ke ci gaba da kokawa.
Domin Kari
No media source currently available