Asabar, Afrilu 30, 2016 Karfe 21:40

  Rumbun Hotuna

  Ziyarar Sojojin Amurka Masu Kula da Harkokin Farar Hula na “Civil Affairs Team"

  Sojojin Amurka sun kawo ziyara Muryar Amurka, inda suka tattauna da shugabannin sashen Afirka na Muryar Amurka, akan yadda harkokin Afirka ke gudana, musamman game da batun taimako wajen yaki da ta’addanci da kuma samar da abubuwan more rayuwa.

  Ziyarar Janar Lamidi Adeoshun a Jamhuriyar Nijar

  Komandan Rundunar Tsaron Kasashen Yankin Tabkin Tchadi Manjo Janar Lamidi Adeoshun ya kawo wata ziyarar aiki a Jamhuriyar Nijar, wanda ya samu ganawa da Shugaban Hafsan hafsoshin Nijar Janar Seyni Garba.

  Samantha Power Ta Gana Da Shugaba Muhammadu Buhari a Najeriya

  Anyi wata ganawa ta musamman tsakanin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da jakadiyar Amurka a Majalisar 'Dinkin Duniya, inda suka tattauna kan muhimman butun yan gudun hijira da yakin Boko Haram.  Sauraron Shari'ar Oscar Pistorius

  A watan Yuni ne za a yankewa tsohon tauraron nan mai gudun Pampalaki, Oscar Pistarius hukunci, bisa laifin kisan budurwarsa, biyo bayan zaman da babbar kotun birnin Pretoria ta yi yau litinin. 18 ga watan Afrilu.


  Shugaba Muhammadu Buhari Na Najeriya A Kasar Sin

  Shugaba Muhammadu Buhari Na Najeriya A Kasar Sin

  Bakin Iyakar Kasar Macedoniyya

  Bakin iyakar kasar Macedoniyya.  Juyayin Mummunan Harin Bam Da Ya Hallaka Jama'a A Pakistan

  Jama'a 72 Ne Suka Rasa Rayukan Su, 300 Kuma Suka Jikkata A Harin Bam Da Aka Kai Yayin Da Suke Gudanar Da Bukukuwan Easter A Pakistan


  Dakarun Najeriya Sun Gano Tarakkan 'Yan Boko Haram A Dajin Sambisa

  Yayin da Sojojin Najeriya ke cigaba da fafarar 'yan boko haram a dajin Sambisa, sun gano wasu abubuwa da mayakan suka boye.

  Wasu Zaratan Sojoji Da Ake Kira Strike Group Team B A Karkashin Shiyya Ta 7 Sun Gano Inda Ake Harhada Bama-Bamai A Kumshe

  Sojojin dake sintiri sun gano wannan masana'antar harhada bama-bamai, manya da kanana a Kumshe, a bayan da suka fatattaki 'yan Boko haram daga wurin.

  Jerin Hotuna: Sojojin Nijar Na Yakar Boko Haram A Yankin Diffa

  Wakilin Muryar Amurka ya gane ma idanunsa yadda sojojin Nijar suke tinkarar 'yan Boko haram a bakin iyakar kasar da Najeriya.

  Audio Shirin Safe:       1530 - 1600 UTC

  Audio Shirin Hantsi:    1530 - 1600 UTC

  Audio Shirin Rana:       1530 - 1600 UTC

  Audio Shirin Dare:       1530 - 1600 UTC

  Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

  Karin Bayani akan Sauti