Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka tayi kira ga shugaban kasar Siriya ya sauka daga karagar mulki


Wata mace cikin masu zanga zanga dauke da tutar kasar Siriya.
Wata mace cikin masu zanga zanga dauke da tutar kasar Siriya.

Amurka tayi kira ga shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad ya sauka daga karagar mulki ba tare da bata lokaci ba, bayan zargin yiwa wani shugaban hamayya kisan gilla.

Amurka tayi kira ga shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad ya sauka daga karagar mulki ba tare da bata lokaci ba, bayan zargin yiwa wani shugaban hamayya kisan gilla.

Sanarwar Fadar White House ta kushe da kakkausar murya, kisan Mashaal Tammo, kakakin jam’iyar makomar Kurdawa da aka fi sani da suna Kurdish Future Party, kuma memban sabuwar kungiyar hamayya ta hadin guiwa a Siriya. ‘Yan gwaggwarmaya sun ce wadansu ‘yan bindiga da suka rufe idanunsu ne suka kashe shi a gidanshi dake garin Qamishli a arewacin kasar jiya Jumma’a.

Fadar White House tayi gargadi da cewa, tilas ne Mr. Assad ya sauka daga karagar mulki yanzu, kafin ya kara jefa kasar cikin yanayi mai hadari.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, hare haren sun nuna yunkurin gwamnatin kasar Siriya na baya bayan nan na murkushe hamayyar lumana da ake yi a Siriya, inda dubban masu zanga zanga suke taruwa domin nuna kin jinin gwamnatin shugaba Bashar al-Assad.

Shugaban adawan yana daga cikin mutane takwas da ake zargin jami’an tsaro da kashewa jiya jumma’a a Siriya,

Tun farko shugaban kasar Rasha Dmitry Medvedev yace Mr. Assad yana bukatar yin garambawul ko kuwa ya yi murabus. Sai dai ya kara da cewa, Rasha tana adawa da yunkurin kasashen ketare na kauda Mr. Assada daga karagar mulki.

XS
SM
MD
LG