Talata, Yuni 30, 2015 Karfe 04:30

Afirka

Akalla Mutane 60 Suka Halaka A Abidjan, A bikin Shiga Sabuwar Shekara.

Mutane suke tsaye a gefen kayayyaki na mutane da suka yi turereniya a daren jiya, a Abidjan.Mutane suke tsaye a gefen kayayyaki na mutane da suka yi turereniya a daren jiya, a Abidjan.
x
Mutane suke tsaye a gefen kayayyaki na mutane da suka yi turereniya a daren jiya, a Abidjan.
Mutane suke tsaye a gefen kayayyaki na mutane da suka yi turereniya a daren jiya, a Abidjan.
Aliyu Imam
 Jami’ai a kasar Cote ‘d Voire sun ce a kalla mutane 60 ne suka mutu bayan da aka sami turereniya a safiyar yau Talata a Abidjan, babban birnin kasar.

Masu agajin gaggawa sunce wasu mutane 200 ne suka jikkata a wanna lamari, wanda ya faru a gundumar da ake kira Flato,wani filin wasa wajenda mutane suka taru domin kallon wasannin kayan wuta na shigar sabuwar shekara.

Tashar talbijin ta AIP a kasar ta bada labarin cewa, galibin wadanda lamarin ya rutsa da su matasa ne. Iyaye wadanda hankalinsu ya tashi sun dunguma zuwa filin wasan domin neman 'yayansu cikin gawarwaki da suke wurin.

Hukumomin kasar sun kaddamar da bincike domin tantance dalilinda ya janyo turereniyar.
An rufe wannan dandalin
Yadda Ake Son Gani
Sharhi/Ra'ayi
     
by: Haruna Ibrahim Daga: Birnin kebbi
10.01.2013 12:01
Allah ya jikan wadanda suka rasu awannan mummu nan cin koso

Audio Shirin Safe:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Hantsi:    1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Rana:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Dare:       1530 - 1600 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Karin Bayani akan Sauti