Jami’ai a kasar Bangladesh sun ce wata gobara data tashi a wata masana’natar dinka suturorin zamani ta kashe akalla mutane 100.
Masu aikin ceto sun gano gawarwakin ne a safiyar yau lahadi.
Hukumomin kasar suka ce gobarar ta barke ne a daren jiya Asabar a masana’anatar da ake kira Tazreen mai hada kayan ado na zamani dake a wajen fitar birnin Dhaka fadar kasar.
Wasu rahotanni suka ce wutar ta rutsa da wasu ma’aikata masu yawa a wasu sassan benaye, kuma wasu sun yi tsalle da nufin tserewa daga wutar.
Ba a san musabbabin tashin gobarar ba.
Ahalinda ake ciki kuma, jami’an ‘yan kwana-kwana anan birnin Washington sun ce mutane uku sun jikkata sakamakon tashin wata gobara a helkwatar ma’aikatar harkokin wajen Amurka.
Kakakin ma’aikatar Victoria Nuland tace gobarar ta tashi ne a safiyar jiya Asabar lokacinda ma’iakata suke gudanar gyare gyare da aka saba yi.
Jami’an ‘yan kwana-kwanan suka ce mutum guda rai na hanun Allah, wasu biyu kuma sun samu rauni masu tsanani.Gobarar ta tashi ne daga hanyoyin samarda iska da kuma hayaki suke bi a gine ginen zamani.
Kakaki Nuland tace nan da nan aka kashe gobarar, kuma tuni aka sake bude ofishin domin cigaba da ayyuka da aka saba yi a karshen mako.