Laraba, Mayu 27, 2015 Karfe 22:35

Afirka

'Yan Gani Kashenin Islama A Mali, Sun Kai KUnar Bakin Wake Irinsa Na Farko

Sojojin Mali suke nazarin wata nakiya da aka gano.Sojojin Mali suke nazarin wata nakiya da aka gano.
x
Sojojin Mali suke nazarin wata nakiya da aka gano.
Sojojin Mali suke nazarin wata nakiya da aka gano.
Aliyu Imam
Sojojin Mali sun ce wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa kansa  kusa da gungun wasu sojoji, wannan shine karo na farko da yan tawayen suka fara amfani da wannan salon kai harin, tun lokacin da Faransa ta daukin matakin soji na kai farmaki kan ‘yan tawayen, cikin watan jiya.

Jami’an sun ce wani soja ya sami rauni lokacin da dan kunar bakin waken ya tunkaro wurin akan babur ya kuma tada nakiyoyin,  a wani wurin da sojojin suke bincike motoci kusa da birni Gao yau jumma’a.

Dakarun faransa masu marawa dakarun Mali baya, suna fuskantar karin turjiya  daga yan tawayen islamar a arewacin Mali a yan kwanakin nan, bayan da dakarun suka kwato iko a yankin a watan da ya gabata.
An rufe wannan dandalin
Sharhi/Ra'ayi
     
Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

Audio Shirin Safe:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Hantsi:    1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Rana:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Dare:       1530 - 1600 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Karin Bayani akan Sauti