Asabar, Fabrairu 13, 2016 Karfe 03:27

  Labarai / Sauran Duniya

  Amurka Ta Soki Shirin Isra'ila Na GIna Sabbin Gidaje A Yankunan Falasdinu.

  Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hilary Clinton da PM Isra'ila Benjamin Netanyahu, a birnin kudus, ranar 20 ga watan jiya.Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hilary Clinton da PM Isra'ila Benjamin Netanyahu, a birnin kudus, ranar 20 ga watan jiya.
  x
  Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hilary Clinton da PM Isra'ila Benjamin Netanyahu, a birnin kudus, ranar 20 ga watan jiya.
  Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hilary Clinton da PM Isra'ila Benjamin Netanyahu, a birnin kudus, ranar 20 ga watan jiya.

  Amurka ta ta soki sanarwar da Isra’ila t bayar na shirin gina gidaje dubu uku ga ‘yan kaka-gida a yammacin kogin Jordan da  kuma a gabshin birnin kudus, bayan nasarar da hukumomi yankin Falasdinu suka samu na amincewar Majalisar Dinkin Duniya.

  Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hilary Clinton, ta fada jiya jumma’a cewa gwamnatin Obama kamar sauran gwamnatocin Amurka da  suka wuce, sun bayyana cewa irin wadannan matakai suna maida hanun agogo baya a yunkurin shawarwarin wanzarda zaman lafiya.

  Clinton tayi magana ne a wani taro da  wata cibiya mai tsara manufofi kan gabas ta tsakiya ta shirya, inda minisocin harkokin wajen Isra’ila da na tsaron kasar Avigdor Lieberman da  Ehud Barak suka halarta.

  Jami’an Isra’ila wadanda suka zanta  da kafofin yada labarai bisa  sharadin ba za a bayyana sunayensu ba, sun ce  gwamnatin PM Benjamin Netanyahu ta bada umurnin a aiwatar da gine ginen, da kuma aikin farko farko na kebe wasu sassa a yammacin na kogin Jordan din.

  Sauti

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  • Yau da Gobe
   Minti 30

   Yau da Gobe

   Yau da Gobe

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye