Talata, Disamba 01, 2015 Karfe 17:28

Labarai / Sauran Duniya

Amurka Tana Daf Da Fadawa Kunci, Idan Ba'a Cimma Yarjejeniya kan.....

Zauren majalisar dokokin AmurkaZauren majalisar dokokin Amurka
x
Zauren majalisar dokokin Amurka
Zauren majalisar dokokin Amurka
Aliyu Imam
Yau litinin, ‘yan majalisar dokokin Amurka zasu sake hallara domin yunkurin karshe  na kuacewa dokar da  zata ayyana Karin kudin haraji da ragin kudaden da Gwamnati ke kashewa domin gudanar da ayyukan yau da kullun.Dokar da zata fara aiki daga gobe daya ga watan Janaiaru na sabuwar shekara.
Tilas ne duk wata yarjejeniyar da aka cimma da farko ta ratsa  ta hanun majalisar dattijai, wacce zata koma zama kamin tsakar ranar litinin din nan, bayan da aka kwashe wunin jiya lahadi ana gudanar da shawarwari masu zurfi, da a karshe basu cimma kome ba.

Mataimakin shugaban Amurka Joe Biden, yayi wata ganawa a kebe tare da jagoran maras rinjaye a majalisar dattawan Amurka Mitch McConnel,a daidai lokacin da hadin gwiwar wakilan jam’iyyun Democrat da na Republican ke kokarin samun daidaituwa domin rage bambance-bambancen dake tsakaninsu game da karin kudin haraji kan masu hanu da  shuni, da kuma zabtarewar da za  ayiwa kudadenda gwamnati take kashewa.

Amma anji shugaban masu rinjaye a majalisar dattawan Amurka Harry Reid yana cewa gibin da yake tsakanin sassan biyu suna  da “muhimmanci kwarai”, yayinda shugaban maras rinjaye Mitch McConnell, yake cewa dan abunda ya rage yana buktar  "karfin hali ko kuma kwarin guiwa” tsakanin wakilan majalisun, domin a cimma daidaito.

Idan har majalisar dattawan wacce ‘yan Democrat suke da rinjaye ta amince da yarjejeniyar, to tilas majalisar wakilai da ‘yan Republican suke da rinjaye ita ma ta kada kuri’ar amincewa da daftarin.  Sannan daga bisani, shugaban kasa ya rattabawa kudurin hanu a maraicen litinin din nan, wanda hakan zai kaucewa dokar da zata kara haraji kusan kan duk wani dan kasar Amurka daga Talata, 1 ga watan Janairu 2013.
An rufe wannan dandalin
Sharhi/Ra'ayi
     
Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

Sauti

 • Yau da Gobe
  Minti 30

  Yau da Gobe

  Yau da Gobe

 • Shirin Rana
  Minti 30

  Shirin Rana

  Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

 • Shirin Hantsi
  Minti 30

  Shirin Hantsi

  Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

 • Shirin Safe
  Minti 30

  Shirin Safe

  Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

 • Shirin Dare
  Minti 30

  Shirin Dare

  A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

Karin Bayani akan Shirya-shirye
Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Shirya-shirye