Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Tana Leken Asiri Kan Kungiyoyin Ta'addanci A Afirka.


Samfurin jiragen yakin Amurka da basu da matuka.
Samfurin jiragen yakin Amurka da basu da matuka.

Jaridar Washington Post wacce ake bugawa anan birnin Washington DC ta buga labarin cewa rundunar sojan Amirka ta kafa kananan sansanonin mayakan sama a wasu sassa nan Afirka domin yiwa kungiyoyin ‘yan ta’ada leken asiri.

Jaridar Washington Post wacce ake bugawa anan birnin Washington DC ta buga labarin cewa rundunar sojan Amirka ta kafa kananan sansanonin mayakan sama a wasu sassa Afirka domin leken asiri kan kungiyoyin ta'adda.

Jaridar ta ambaci jami’an Amirka dana Afrika suna fadin cewa tun shekara ta dubu biyu da bakwai aka kafa sansanoni a kasashe Afrika da dama. Kasashen sun hada harda Burkina Faso, da Uganda da Ethiopias da Djibouti da Kenya da kuma Seychelles.

Rahoton yace maimakon amfani da jiragen saman leken asiri wadanda babu matuka a ciki, shirin yana amfani da jirgin sama mai inji guda samfurin PC-12 wadanda kuma suke da matuka. Rahoton yace wadannan kanana jiragen saman leken asirin suna da naurar daukan hoton vidiyo da na’urar bin diddigi da kuma samun bayanai wayoyin celula da bayana gidajen rediyo.

Amurka tana auna leken asirin ne kan 'yan yakin sa kai wadanda aka danganta da kungiyar Al Qaida a Somaliya, da Yamal da kuma kungiyar yan tawayen Lords Resistance Army a tsakiyar Afrika.

Jaridar Washington Post ta buga wannan labari ne bisa rahotanin baya bayanan da ta samu daga jami’an soja da jami’an gwamnati wadanda ba’a baiyana sunayensu ba da kuma bayanai kwangilar wannan aiki dana kafofin diplomasiya da Wikileaks ya kwarmata.

XS
SM
MD
LG