Litinin, Fabrairu 08, 2016 Karfe 02:50

  Labarai / Sauran Duniya

  Amurka Tana Son A ladabtar Da Koriya Ta Arewa Sabo Da Harba Roka

  Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Susan Rice take magana da manema labarai kan Koriya Ta Arewa, ranar Laraba.Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Susan Rice take magana da manema labarai kan Koriya Ta Arewa, ranar Laraba.
  x
  Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Susan Rice take magana da manema labarai kan Koriya Ta Arewa, ranar Laraba.
  Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Susan Rice take magana da manema labarai kan Koriya Ta Arewa, ranar Laraba.
  Aliyu Imam
  Amurka tace tana son ganin an dauki “matakan ladabtarwa” kan Koriya ta Arewa sabo da harba roka data yi, domin haka Washinton ta ci gaba da  cewa, zata bukaci kasa da kasa ta dauki mataki cikin kwanaki masu zuwa.

  Jiya laraba, kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah wadai da harba rokar, ya kira matakin,a fili yake cewa hakan ya kaucewa kudurin majalissr dinkin duniya, wanda ya haramtawa Pyongynag aiwatar da duk wani irin gwaji na makamai masu  linzami dana Nukiliya.

  Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Susan Rice, tace sanarwar da ta fito daga kwamitin itace wacce kwamitin ya bayar ba tare da bata wani lokaci kuma mai karfin gaske da kwamitin mai wakilai 15 ya bayar.Madam Rice tace Amurka zata yi aiki da hukumomin kasa da kasa domin cimma matsaya kan mataki da ya kamata a dauka kan Koriya ta Arewa. Tace zata duba gurori masu ma’ana a zahiri da zasu hada da ladabtarwa.

  Haka kuma Rice tace, matakin da  Koriya Ta Arewa ta dauka, a fili ya jawo shakku kan dukufar kasar na komawa kan teburin shawarwari, da suka kunshi  kasashe shida dangane da  shirin nukiliyar kasar.

  Ranar laraba, Koriya Ta Arewa ta bada sanarwar ta chulla roka mai cin dogon zango, wacce kasar tace ta kunshi tauraruwar dan Adam da zai rika kewaya duniya.

  Sauti

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye