Alhamis, Yuli 02, 2015 Karfe 00:11

Afirka

Amurka zata mikawa Afrika ta Kudu aikin yaki da cutar kanjamau

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary ClintonSakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton
x
Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton
Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton
Sakatariyar ma’aikatar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton tace Washington ta fara mikawa Afrika ta Kudu ikon gudanar da ayyukan yaki da cutar kanjamau, kasar da tafi kowacce a duniya yawan wadanda ke dauke da kwayar cutar HIV.
Clinton ta sanar da haka ne yau Laraba yayin jawabinta a jami'ar Western Cape dake bayan garin birnin Cape Town. Ta bayyana cewa, yarjejeniyar wani gagarumin ci gaba ne a yaki da cutar kanjamau.

Amurka ta rage yawan kudin da take badawa na yaki da cutar kanjamau zamanin shugaba Thabo Mbeki wanda ya musanta cewa, akwai dangantaka tsakanin kwayar cutar HIV da cutar kanjamau, ya kuma ki amincewa da magungunan jinyar cutar da kasashen duniya suka yi na’am da shi.

Washington ta kashe dala biliyan uku da miliyan dubu dari biyu, tun daga shekara ta dubu biyu da hudu, kan ayyukan yaki da cutar kanjamau a Afrika ta Kudu. Ko da yake kasar ta taka rawar gani a wajen rage yada cutar, sama da kashi goma sha bakwai bisa dari na al’ummar kasar suna dauke da kwayar cutar HIV
An rufe wannan dandalin
Yadda Ake Son Gani
Sharhi/Ra'ayi
     
by: Luka Kefas Daga: Jos. Naijeriya
14.08.2012 17:17
Ra'ayi ta game da gudanar da mulki a kasar Naijeriya itace shugabanni mu su nuna adalci wa takawa.

Audio Shirin Safe:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Hantsi:    1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Rana:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Dare:       1530 - 1600 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Karin Bayani akan Sauti