Talata, Yuni 30, 2015 Karfe 04:30

Afirka

.'Yan Tawayen M23 Sun Fara Shawarwarin Sulhu Da Gwamnatin Kwango

'Yan tawayen kungiyar M23 suke jigilar kaya'Yan tawayen kungiyar M23 suke jigilar kaya
x
'Yan tawayen kungiyar M23 suke jigilar kaya
'Yan tawayen kungiyar M23 suke jigilar kaya
An fara shawarwarin sulhu tsakanin ‘yan tawayen kungiyar M23 da kuma jami’an gwamnatin kasar Kwango Kinshasa.

An fara shawarwarin jiya lahadi a Kampala babban birnin Uganda cikin wani yanayi na tankiya, a bayanda wakilin kungiyar ‘yan tawaye ta M23, Francosi Ruchongoza, yayi zargin cewa fitinar ta taso ne saboda rashin shugabancin kwarai.

Amma ministan harkokin wajen Kwango Raymond Tshibanda, wanda ya wakilici gwamnati, ya bayyana rashin jin dadin kalaman.

A makon jiya ne kungiyar ‘yan tawayen ta M23 ta janye daga birnin Goma, amma tayi gargadin cewa zata sake kama shi muddin gwamnati bata fara shawarwarin sulhu da ita kamar yadda tayi alkawari tunda farko ba.

A halinda ake ciki kuma, dakarun gwamnatin Somalia da sojojin kiyaye zaman lafiya na tarayyar Afirka sun kwace garin Jowhar daga hanun mayakan sakai na al-shabab.
Shaidun gani da ido suka ce a jiya lahadi da  safe ne dakarun suka shiga garin suka gwabza dan karamin fada da mayakan sakan, daga bisani suka kama garin baki daya.
An rufe wannan dandalin
Sharhi/Ra'ayi
     
Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

Audio Shirin Safe:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Hantsi:    1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Rana:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Dare:       1530 - 1600 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Karin Bayani akan Sauti