Jumma’a, Nuwamba 27, 2015 Karfe 16:20

Labarai / Sauran Duniya

An Kashe Jakadan Amurka A Kasar Libya

An kashe jakada Chris Stevens tare da wasu jami'an jakadanci uku a farmakin da aka kai kan karamin ofishin jakadancin Amurka dake birnin Benghazi

Wani dan zanga-zanga a kofar karamin ofishin jakadancin Amurka dake cin wuta a Benghazi a kasar LibyaWani dan zanga-zanga a kofar karamin ofishin jakadancin Amurka dake cin wuta a Benghazi a kasar Libya
x
Wani dan zanga-zanga a kofar karamin ofishin jakadancin Amurka dake cin wuta a Benghazi a kasar Libya
Wani dan zanga-zanga a kofar karamin ofishin jakadancin Amurka dake cin wuta a Benghazi a kasar Libya
An kashe jakadan Amurka a kasar Libya tare da wasu ma’aikatan jakadanci guda uku, a bayan da gungun mutane suka abka cikin karamin ofishin jakadancin Amurka dake birnin Benghazi na gabashin kasar jiya talata da maraice.

‘Yan zanga-zangar da aka ce sun fusata da wani fim na batunci ga Annabi Muhammad (saw) wanda wani mutumin da ba kwararre ba ya hada shi a nan Amurka, sun yi harbi a kan karamin ofishin jakadancin na Amurka dake Benghazi, suka kuma cinna masa wuta.

Jakada J. Christopher Stevens shi ne jakadan Amurka na farko da aka kashe a wata kasar waje a cikin shekaru fiye da 20. Shi kwararre ne a fannin huldar Amurka da kasashen waje, kuma yana daya daga cikin jakadun Amurka da suka fi kwarewa kan harkokin wannan yanki. A cikin watan Mayu ya kama aiki a birnin Tripoli.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta bayar da rahoton cewa jami’in kula da harkokin yada labarai Sean Smith na cikin wadanda aka kashe. Sakatriyar harkokin waje Hillary Clinton ta ce har yanzu su na kokarin sanar da iyalan sauran jami’an guda biyu kafin a bayyana sunayensu.

A yau laraba, shugaba Barack Obama yayi Allah wadarai da kisan Amurkawan su hudu.

Shugaban ya fada a cikin wata sanarwa cewa mutanen hudu, misali ne na kudurin Amurka na wanzar da ‘yancin walwala, da adalci da kuma kawance da kasashe tare da jama’a a fadin duniya,l yana mai fadin cewa, rayuwarsu ta sha bambam, a fili, da irin ta mutanen da suka hallaka su.

Shi ma mukaddashin firayim ministan Libya, Mustafa Abu Shagour, yayi Allah wadarai da kisan jami’an jakadancin hudu na Amurka, yana mai bayyana wannan a zaman aiki na ragwanci.

‘Yan tawayen kasar Libya su na kaunar Stevens sosai a sabvoda irin goyon bayan da ya bayar ga tunzurin da suka yi har suka kawar da shugaba Muammar Gaddafi daga kan mulki.
An rufe wannan dandalin
Yadda Ake Son Gani
Sharhi/Ra'ayi
     
by: Abubakar lawal zube Daga: Kastina Nijeriya
13.09.2012 07:29
Barkan ku da war haka duk da cewa daukar doka a hannu bata dace ba saboda wannan jakada ne kuma a dokar musulunci ba'a ka she jakada. A lokaci guda ba zamu boye bakin ciki da damuwa a kan abinda aka yi mana a wannan kasa kuma muna sauraron abinda mahunkuntanta zasu ce

Sauti

 • Shirin Rana
  Minti 30

  Shirin Rana

  Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

 • Shirin Hantsi
  Minti 30

  Shirin Hantsi

  Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

 • Shirin Safe
  Minti 30

  Shirin Safe

  Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

 • Shirin Dare
  Minti 30

  Shirin Dare

  A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

 • Yau da Gobe
  Minti 30

  Yau da Gobe

  Yau da Gobe

Karin Bayani akan Shirya-shirye
Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Shirya-shirye