Talata, Yuni 30, 2015 Karfe 22:24

Afirka

Shugaba Ernest Bai Korma yayi rantsuwar kama aiki a wa'adi na biyu.

Shugaba Ernest Bai Koroma yake daga hanu ga magoya bayansa a Freetown.Shugaba Ernest Bai Koroma yake daga hanu ga magoya bayansa a Freetown.
x
Shugaba Ernest Bai Koroma yake daga hanu ga magoya bayansa a Freetown.
Shugaba Ernest Bai Koroma yake daga hanu ga magoya bayansa a Freetown.
Aliyu Imam
An rantsarda shugaban kasar Saliyo Ernest Bai Koroma, domin fara mulki wa’adi na biyu, bayan da hukumar zaben kasar ta ayyana shi a zaman  wanda ya lashe zaben kasar da  aka gudanar cikin makon jiya.

Da yake jawabi ga dumbin magoya bayansa dake sowa jiya a jumma’a a birnin Freetwon, shugaba Koroma yayi alkwarin zai yaki cin hanci da  rashawa, kuma zai jawo hankalin masu zuba jari daga ketare su zo kasar domin zuba jari.

An rantsarda shugaban kasar ne sa’o’I kadan bayanda shugabar hukumar zaben kasar Chrisitina Thorpe, ta bada snaarwar cewa Mr. Koroma ya sami nasarar a sake zabensa da kashi 58 cikin dari na kuri’u da  aka kada.

Shugaba Koroma ya kara da waasu ‘yan takara takwas, kuma doka ta bukaci ya sami kashi 55 cikin dari domin kaucewa a yi zaben fidda gwani.Babban abokin hamayyar Mr. Koroma Julius Ma’ada Bio, ya sami kashi 37 cikin dari na kuri’u da  aka kada.

Har yanzu hukumar zabe bata bayyana sakamakon zaben majalisar dokoki da aka gudanar lokaci daya da zaben shugaban kasar ranar 17 ga watan nan ba.

Jami’an hukumar zaben sun ce mutane masu yawan gaske ne suka fito domin zaben da aka yi, kuma masu aikin sa ido sun ce an gudanar da zaben cikin lumana kuma babu kumbiya-kumbiya.

Zaben shine karo na uku da  ake gudanar da zabe a saliyo tun bayan da aka kawo karshen yakin basasar kasar a 2002.
An rufe wannan dandalin
Sharhi/Ra'ayi
     
Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

Audio Shirin Safe:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Hantsi:    1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Rana:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Dare:       1530 - 1600 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Karin Bayani akan Sauti