Asabar wasu shugabnnin Afirka sun yi taro da nufin warware rikicin ‘yan tawayen a jamhuriyar demokuradiyyar kwango, suka yi kira ga ‘yan tawayen su “dakatar da duk wata harkar yaki”, kuma su janye daga birnin Goma mai muhimanci da suka kama a farkon makonnan.
Sanarwar da shugabannin suka bayar a jiyan, ta kuma yi kira ga ‘yan tawayen su bar zancen kifar da gwamnatin kwangon.
Shugabannin kasashen Uganda, da Kenya, da Tanzania, da kuma na jamhuriyar Demokuradiyyar kwango ne suka gana a Kampala babban birnin Uganda, amma takwaranso daya wanda yake da muhimmanci da bai sami halarta ba shine shugaban Rwanda paul Kagame, wanda ya soke zuwa a kurarren lokaci, ya tura ministan harkokin wajen kasar a madadin kansa.
Majalisar Dinkin Duniya ta zargi Rwanda cewa tana goyon bayan kungiyar ‘yan tawaye da ake kira M23 a jamhuriyar ta kwango, zargind huku8momin kasar suka musanta.
'Yan tawayen Kwango a garin Sake a lokacinda suke sintiri.x
'Yan tawayen Kwango a garin Sake a lokacinda suke sintiri.
Taron kolin da shugabannin suka yi a kampala yazo ne a dai dai lokacind aake nuna damuwa kan dannawar da ‘yan tawayen suke yi zuwa gabasghin kwango, da kuma canji da aka samu a rundunar mayakan kasar.
Shugaban kasar Kwango Joseph Kabila ya dakatar da babban hafsan hafsoshin kasar Janar Gabriel Amisi kan zargin yana sayarwa ‘yan tawaye a gabashin kasar makamai.
Dakatarwar da aka yi wa janar Amisi tazo ne kwanaki uku bayan da dakarun ‘yan tawaye suka sami nasara kan sojojin kwango suka kama birnin Goma.