Lahadi, Mayu 01, 2016 Karfe 08:59

  Labarai / Sauran Duniya

  Ana ci gaba da gumurzu a kasar Siriya

  wadansu mata da aka kai hari a unguwarsuwadansu mata da aka kai hari a unguwarsu
  x
  wadansu mata da aka kai hari a unguwarsu
  wadansu mata da aka kai hari a unguwarsu
  ’Yan gwaggwarmayar kasar Siriya sun ce dakarun shugaba Bashar al-Assad sun bude wuta a wadansu sassan babban birnin kasar da kuma birnin Aleppo inda ake fama da tashin hankali yau jumma’a, kwana daya bayanda Majalisar Dinkin Duniya ta dauki matakin kawo karshen aikin gani da ido da take yi a kasar.

  Kungiyar kare hakkin bil’adama kan harkokin kasar Siriya dake da zama a Birtaniya ta kuma bada labarin arangama tsakanin dakarun gwamnati da ‘yan tawaye kusa da babbar tashar jirgin saman sojin kasar dake Damascus.

  Rami Abd-al-Rahman, darektan cibiyar sa idon ta Birtaniya ya shaidawa Muryar Amurka cewa, tashin hankali na baya bayan nan ya auku ne bayan kashe a kalla mutane 180 jiya a duk fadin kasar. Yace an sami gawarwakin wadansu mutane 65 da ba a tantance ba, a garin Qatana dake kudu maso yammcin birnin Damascus.

  Jiya alhamis, kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya sanar da cewa, zai bar wa’adin aikin masu gani da ido a Siriya ya cika. Ranar Lahadi ne wa’adin yake cika, sai dai kwamitin Sulhu yace yana kyautata zaton kafa ofishi a kasar da yaki ya daidaita.

  Shugaban Kwamitin a halin yanzu, jakaden kasar Faransa, Gerard Araud yace, membobin kwamitin sun amince da cewa, ba a cika sharudan da aka gindaya da zai bada damar ci gaba da aiki a kasar ba.

  Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa, kimanin Siriyawa miliyan biyu da dubu dari biyar suna bukatar agaji sabili da tashin hankalin da aka shafe watanni goma sha takwas ana yi na nuna kin jinin Mr. Assad.

  Watakila Za A So…

  Obama Ya Halarci Taron Cin Abincin Dare Na Karshe Na KUngiyar 'Yan Jarida

  Wannan shine karo na takwas kuma na karshe da 'yan jarida masu aiki a fadar white suka a zamanin mulkin Obama Karin Bayani

  Za'a Iya Dasa Kan-Dan-Adam Kan Wata Gangar Jiki?

  Wasu likitoci suka ce wannan hauka ne kawai, kuma ba zai yi aiki ba. Karin Bayani

  Zika Ta Kashe Mutum Na Farko A Amurka.

  Mutumin dan shekaru 70 da haifuwa a watan febwairu ne ya kamu d a cutar da Zika. Karin Bayani

  A Kenya Wani Gini Mai Hawa 7 Ya Fadi Da Mutane A Ciki.

  Ambaliyar ruwa ne ya janyo faduwar ginin dake wata unguwar marasa galihu. Karin Bayani

  Sauti Najeriya Ba Zata Kara Kashe Kudi Ba Don Nemawa Jami’anta Magani A Kasar Waje

  Duk da yake kowanne dan kasa na da ‘yancin fita domin neman waraka daga cutar dake damunsa, babban abin takaici inji shugaban Najeriya Mohammadu Buhari, a ta bakin ministan lafiya, shine yadda yan kasar ke yin tururuwa a kasashen waje domin neman maganin rashin lafiya. Karin Bayani

  Sauti

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye