Alhamis, Satumba 03, 2015 Karfe 20:11

Labarai / Sauran Duniya

Ana Harsashen Cewa Shugaba Obama Ya Kada Abokin Takararsa Mitt Romney

Hasashe ya nuna cewa shugaban Amurka Barack Obama ya kada abokin takararsa na jam’iyyar Republican Mitt Romney.

Magoya bayan shugaba Obama suna murna bayan da sakamako ya yi nuni da cewa ya lashe zabe
Magoya bayan shugaba Obama suna murna bayan da sakamako ya yi nuni da cewa ya lashe zabe

Hasashe ya nuna cewa shugaban Amurka Barack Obama ya kada abokin takararsa na jam’iyyar Republican Mitt Romney.

Magoya bayan shugaban kasar a shelkwatar yakin neman zabensa dake Chicago suna kada totuci suna sowa a cikin daren jiya talata, lokacinda suka sami labarin, bayanda  shugaban ya lashe jihohi da dama wadanda suka bashi kuri’u metan da 70 da  ake bukata na wakilai masu zaben shugaban kasa.

Wani ma’aikacin yakin neman sake zaben shugaban kasa, ya rubuta a dandalin Twitter cewa “karin wasu shekaru hudu tare da hoton shugaba Obama ya rungumi uwargidansa Michelle Obama. Gini mafi tsawo a birnin New York da ake kira Empire state ya haska fitila mai launin ruwan zargina launin jam’iyyar Democrat.

Hasashe na baya bayannan ya nuna shugaba Obama ya sami kuri’a 275 na wakilai masu zaben shugaban kasa, yayinda Mitt Romney yake da 203.

Hasashen ya nuna shugaba Obama ya sami nasara a gundumar Columbia da jihohi 20 ciki harda  inda aka yi karon batta watau jihohin Ohio, Iowa, New Hampshirwe, da kuma Pennsylvania. Mr. Romney ya sami nasara  a jihohi 23 ciki harda  jihar Carolina ta arewa, da Indiana, wacce shugaba Obama ne ya lashe shekaru hudu da suka wuce. A halin yanzu yana da wuya ace ga gwani a jihohin Florida da Virginia, cikin jihohi da jam’iyun biyu suka fi maida hankali akai.

Jiya talata ‘yan takarar biyu suka kara daukan matakan neman goyon bayan masu zabe yayinda masu kada kuri’a suke tsatstsaye a cikin dogayen layi. An bada labarin fuskantar matsaloli nan da can, kuma duka jam’iyun biyu suka tura lauyoyinsu domin sa ido kan zaben.

Audio Shirin Safe:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Hantsi:    1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Rana:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Dare:       1530 - 1600 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Karin Bayani akan Sauti