Laraba, Mayu 04, 2016 Karfe 16:23

  Labarai / Sauran Duniya

  Saura Kwana Hudu Kafin Zabe: Me 'Yan Takarar Shugabancin Amurka Suke Cewa Ne?

  Shugaban Amurka Brack Obama da uwargidansa Michelle, da kuma abokin takararsa Mitt da Ann Romney.Shugaban Amurka Brack Obama da uwargidansa Michelle, da kuma abokin takararsa Mitt da Ann Romney.
  x
  Shugaban Amurka Brack Obama da uwargidansa Michelle, da kuma abokin takararsa Mitt da Ann Romney.
  Shugaban Amurka Brack Obama da uwargidansa Michelle, da kuma abokin takararsa Mitt da Ann Romney.
  Aliyu Imam
  Shugaban Amurka Barack Obama ya koma fagen yakin neman a sake zabensa, bayan mako daya yana jagoran shirye shiryen gwamnatin tarayya dangane da bala’in guguwar “Sandy.”
  Shugaban dan jam’iyyar Democrat, ya yi yakin neman zabe a jihohin Wisconsin, da Nevada, da Colorado jiya Alhamis. Jihohi uku da suka cikin rukunin jihohi da ake yiwa lakabin “mazari”, wadan nan jihohi duk wanda ya sami nasara a cikinsu, zai lashe zaben shugaban kasa da za a yi ranar Talata.
  Shugaba Obama da abokin takararsa Mitt Romney a wani zaman muhawara da suka yi.Shugaba Obama da abokin takararsa Mitt Romney a wani zaman muhawara da suka yi.
  x
  Shugaba Obama da abokin takararsa Mitt Romney a wani zaman muhawara da suka yi.
  Shugaba Obama da abokin takararsa Mitt Romney a wani zaman muhawara da suka yi.

  Mr. Romney yayi yakin neman zabe a jihar Virginia, daya daga cikin jihohin da suke da muhimmancin gaske a zaben da za a yi ranar 6 ga wata.

  ‘Yan takaran duka biyu sun caccaki shiryen shiryen juna na inganta tattalin arzikin Amurka wanda ahalin yanzu bashi da kwari.Mr. Romney ya gayawa magoya bayansa a Roanoke cewa, ‘yan tsaka-tsaki suna fuskantar matsin rayuwa na kudi a mulkin shugaba Obama. Yace samu ya ragu, yayinda bukatun yau da kullum kamar mai da kiwon lafiya farashinsu sun karu.

  Da yake magana  ga magoya bayansa a Las Vegas, a jihar Nevada shi kuma, shugaba Obama ya gayawa magoya bayansa cewa, shirye- shiryen tattalin arziki da Mr. Romney yake tallatawa, masu hanu da shuni ne zasu fi amfana karkashin shirin, manufofi da yace sun gaza a baya. Shugaban ya kwabi abokin hamayyarsa sabo da gabatar da wadan nan manufofi a matsayin “canji”.

  Jiya Alhamis, magajin garin New York Michael Bloomberg, ya bayyana goyon bayansa ga shugaba Obama a yunkurin shugaban na neman wa’adi na biyu. Magajin garin ya ambaci kokarin Mr. Obama na yaki da gurbatar yanayi, daga motoci da masana’antu. Masana kimiyya sun ce hayaki daga motoci suna taimakawa wajen jawo dumamar yanayi, watakil harda irin mahaukaciyar guguwarda da tayi barna a baya-bayan nan, watau Sandy.

  Shugaba Obama yace goyon bayanda magajin garin ya bashi babbar karramawa ce. Mr. Obama yace kodasahike ra’ayinsu bai zo daya ba kan ko wani lamari, duk da haka dukkansu biyu suna goyon bayan inganta ilmi, garambawul ga shirin shige da fice, da kuma yaki da  sakewar yanayi.

  Watakila Za A So…

  Sauti Tallafin Man Fetur Baya Cikin Kasafin Kudin Bana

  Ministan Mai ya kawo wani tsari ne na yin amfani da yadda ake sayar da danyen Mai a daidaita da yadda ake sayan fetur a Najeriya Karin Bayani

  Sauti Albani akan sugabancin Buhari

  Marigayi Shaikh Muhammad Awal Albani ya yi furuci akan shugabancin Buhari tun kafin ma a zabeshi, abun da yau ya zama tamkar duba Karin Bayani

  Nasarar Trump a Indiana ta sa Cruz janyewa daga takarar shugaban kasa a jam'iyyar Republican

  Senata Ted Cruz, mai wakiltar jihar Texas a majalisar dattawan Amurka ya janye daga takarar shugabancin Amurka, bayanda attajirin nan Donald Trump yayi masa mummunar kaye a zaben fidda gwani da aka yi a jihar Indiana, jiya Talata. Karin Bayani

  'Yan jarida na fuskantar barazana ga aikinsu da rayuwarsu a Sudan ta Kudu

  Jiya Talata da aka yi bikin ranar 'yan jarida ta duniya rahotanni sun nuna cewa Sudan ta Kudu ita ce kasa ta 140 cikin 180 a duniya kan 'yancin aikin jarida musamman wurin neman tantance labari daga jami'an gwamnati Karin Bayani

  Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai zauna yau akan rikicin Syria

  Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ko MDD zai zauna yau da rana domin ya saurari bayanai dangane da halin da ake ciki a Syria, bayan da aka kwashe mako da barkewar sabuwar tarzoma, musamman a birnin Aleppo,birni na biyu a kasar. Karin Bayani

  Farmakin ISIS kan kurdawa a Iraqi ya halaka jami'in sojin Amurka daya

  Amurka da kawayenta suna tsammanin irin farmakin da mayakan ISIS suka kaddamar jiya Talata a a rewacin Iraqi, suka wargaza kan mayakan kurdawa da ake kira Peshmerga na wani dan gajeren lokaci, al'amari da ya janyo mutuwar sojan Amurka na musamman daya. Karin Bayani

  Sauti

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shrin Safe
   Minti 30

   Shrin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  • Yau da Gobe
   Minti 30

   Yau da Gobe

   Yau da Gobe

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye