Jumma’a, Nuwamba 27, 2015 Karfe 09:12

Labarai / Sauran Duniya

Hukumomin Tsaro A pakistan Suna Fuskantar Zargin Kasa Hana Kai Hare-Haren Ta'addanci.

Mazauna birnin Quetta suke duba baraguzan gine gine da harin bam a wata kasuwa ya rusa ranar Asabar.Mazauna birnin Quetta suke duba baraguzan gine gine da harin bam a wata kasuwa ya rusa ranar Asabar.
x
Mazauna birnin Quetta suke duba baraguzan gine gine da harin bam a wata kasuwa ya rusa ranar Asabar.
Mazauna birnin Quetta suke duba baraguzan gine gine da harin bam a wata kasuwa ya rusa ranar Asabar.
Aliyu Imam
Gwamnan lardin Baluchistan yana caccakar jami’an tsaron kasar saboda kasa hana kai harin da aka kai jiya Asabar wanda aya kashe akalla mutane 80, ya jikkata wasu fiye da dari.

Gwamnan lardi Zulfiqar Magsi ya fada yau lahadi cewa kodashike an sakarwa jami’an tsaron kasar mara kan yadda suke gudanar aiki kan kungiyoyin masu tsatstsaran ra’ayi, sun gaza ganowa da wargaza  irin wannan hari da aka kai jiya Asabar a wata kasuwa da take cike makil da mutane.

Haka ma masu zanga zanga sun cika titunan birnin na Quetta, da Karachi dake kudancin kasar, harda Islamabad babban birnin kasar, suna neman da gwamnati ta dauki mataki.

Fashewar wacce ta auku babban birnin lardin Quetta an  auna shi kan ‘yan tsiraru da ake kira Hazara, wadanda ‘yan shi’a ne da suka zauna a lardin Baluchistan  bayan sun kaura daga Afghanistan fiye da shekaru dari da suka wuce.

Kungiyar mayakan sakai da ake kira Lashkar e-Jaghvi ta sdauki alhakin kai harin da ma wani da aka cikin watan jiya wanda ya halaka mutane 90.
An rufe wannan dandalin
Sharhi/Ra'ayi
     
Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

Sauti

 • Shirin Hantsi
  Minti 30

  Shirin Hantsi

  Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

 • Shirin Safe
  Minti 30

  Shirin Safe

  Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

 • Shirin Dare
  Minti 30

  Shirin Dare

  A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

 • Yau da Gobe
  Minti 30

  Yau da Gobe

  Yau da Gobe

 • Shirin Rana
  Minti 30

  Shirin Rana

  Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

Karin Bayani akan Shirya-shirye
Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Shirya-shirye