Jumma’a, Agusta 28, 2015 Karfe 01:12

Labarai / Sauran Duniya

Wani Ba-Amurke Ya Lashe Tambolar Dala Milyan 337

Wani kanti yake tallar tambola mai tsoka a jihar New Jersey.
Wani kanti yake tallar tambola mai tsoka a jihar New Jersey.
Aliyu Imam
Jumma’a, wani dan shekaru 44 da haifuwa, a jihar Michigan dake arewacin Amurka, ya gabatar da kansa a matsayin mutuminda ya lashe tambola mafi tsoka na uku a duk tarihin tambolar da ake kira Powerball.

Donald Lawson wadda yake aikin injiniya na jiragen kasa, yayi ritaya, bayanda ya tabbatar cewa shine ya sami nasarar cin tambolar na dalar Amurka milyan 337. Saboda hakama ya sa wasu daga ‘yan uwansa suma suka yi ritaya  domin  yana son  ya raba arzikin tareda su.

Lawson ya tsaida shawarar  karbar dala milyan 158.7 lokaci daya, maimakon jira shekara da  shekaru domin  ya karbi kudaden baki dayansu watau dala milyan 337 kamin a cire  haraji.

Lawson wanda ya shiga sahun masu arzikin milyan yace rayuwars a zata “inganta”, duk da  haka yace yana shirin ci gaba da rayuwarsa a saukake, wadda yace zai hada da zuwa wurin cin abincin zamanin nan d a ake kira McDonalds.

Lawson ya sayi tikitin tambolar  ne a wani gidan mai, kuma shi da kansa ya zabi lambobin shida, maimakon barin na’ura ta zaba masa.
An rufe wannan dandalin
Sharhi/Ra'ayi
     
Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

Audio Shirin Safe:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Hantsi:    1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Rana:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Dare:       1530 - 1600 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Karin Bayani akan Sauti