Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Zata Kashe Dala Miliyan 4 Don Kawar Da Gubar Dalma


Wadansu kananan yara a kauyen Yangalma, inda aka fi samun yaran da suka kamu da cutar gubar dalma a Jihar Zamfara.
Wadansu kananan yara a kauyen Yangalma, inda aka fi samun yaran da suka kamu da cutar gubar dalma a Jihar Zamfara.

Sai dai ana ta bayyana fargabar ko kamar ayyukan gwamnati da aka gani a can baya, jami'ai zasu handame kudaden ko zasu bari ayi aikin ceto rayuka

Gwamnatin Najeriya tana shirin fitar da kudi fiye da dala miliyan 4 domin tsabtace wurin da aka samu bullar gubar dalma mafi muni a tarihin wannan zamanin a Jihar Zamfara.

A cikin watan Yuni ne gwamnatin Najeriya ta yi alkawarin fitar da wannan kudi domin katse dalmar da ta kashe daruruwan yara, yayin da har yanzu wasu dubbai suke kwance a asibiti.

Sai dai kuma, mutane da dama su na bayyana fargabar cewa kamar yadda aka saba gani a can baya, haka jami’an gwamnati zasu warwashe wannan kudi. Ivan Gayton, shi ne shugaban kungiyar agajin likitoci mai suna Doctors Without Borders a Najeriya. Ya ce, "Kowa a Najeriya ya ga yadda shirye-shirye da ake gabatarwa suke lalacewa a saboda jami’an gwamnati sun handame kudaden. Ina fata a cikin zuciyata cewa hakan ba zai faru a wannan karon ba, domin wannan lamari ba na wasa ba ne."

Shugaban kungiyar likitocin yace wasu dubban yara su na iya shakar wannan guba ta dalma, su mutu, ko kuma kwakwalwarsu ta tabu idan har ba a samu nasarar wannan aikin ba.

A ‘yan shekarun da suka shige, farashin gwal ya tashi a kasuwannin duniya, abinda ya ninka kudin shigar da kananan masu hakar gwal suke samu a Zamfara, ya kuma kara farin jinin wannan aiki, duk da mummunan hatsarin dake tattare da shi.
XS
SM
MD
LG