Asabar, Mayu 30, 2015 Karfe 11:21

Afirka

Kungiyae ECOWAS Ta yi Taro Kan Rikicin Mali Da Guinea.

Taron Koli na kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin AfirkaTaron Koli na kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka
x
Taron Koli na kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka
Taron Koli na kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka
Ministocin tsaro da na harkokin  waje daga kasashe dake yammacin Afirka sunyi wanin taro jiya litinin domin tsara lokaci da kuma hanyoyin taimakawa Mali, inda mayakan sakai masu da’awar su masu kishin Islama suka kama arewacin kasar.

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashe dake yammacin Afirka tana kokarin kawo karshen rikicin siyasa a Mali da kuma Guniea Bissau, inda  aka yi juyin mulki cikin watan Afrilu.

Shugabannin sunyi taron ne a Abidjan babban birnin kasar Ivory Coast, domin nazarin bukatar  da shugaban wucin gadi na Mali Doucounda Traore, ya gabatarwa kungiyar, na neman taimakon soja domin kasar ta yaki masu kishin Islama ta kwace arewacin kasar.

Mali ta nemi a taimaka mata da jiragen yaki da hanyoyin sadarwa, amma bata nemi sojoji ba.
Gabannin a yi wannan taro, kakakin kungiyar ECOWAS Sonny Ugoh, yace kungiyar tana dakon taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan Mali, gabannin ta tsaida lokacinda zata tura sojoji zuwa Mali.
An rufe wannan dandalin
Sharhi/Ra'ayi
     
Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

Audio Shirin Safe:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Hantsi:    1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Rana:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Dare:       1530 - 1600 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Karin Bayani akan Sauti