Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sandan Afirka Ta Kudu Sun Fatattaki Masu Zanga-Zanga


‘Yan sandan Afirka ta Kudu sun jefa barkonon tsohuwa, da harsashin roba da kuma gurnetin tsoratarwa don tarwatsa masu zanga-zanga daura da wata mahakar ma’adanai mallakar wani hamshakin mai sarrafa karfen platinum.

Tashin hankalin da aka yi yau Laraba a Rustenburg, a harabar mahakar ma’adanai mallakar ‘wani kamfanin Ingila da Amurka mai suna Amplats ya janyo fargabar cewa har yanzu fa zanga-zanga a bangaren mahakar ma’adanai ba ta lafa ba.

‘Yan sa’o’i kafin nan, mahakar ma’adanan platinum ta Lonmin ta amince ta bai wa ma’aikatanta karin albashi mai yawa bayan mummunar zanga-zanga ta tsawon sati biyar wadda a ciki aka kashe mutane 45.

Mai magana da yawun ‘yan sanda Dennis Adrio yace masu zanga-zangar na Rustenburg sun taru ba da izini ba a kuma wurin da bai dace ba. Yace ‘yan sanda sun dau matakin ne bayan da su ka yi biris da umurnin su watse.

Sashen hakar ma’adanan Afirka ta kudu shi ne mafi girma a nahiyar Afirka.
XS
SM
MD
LG