Litinin, Nuwamba 30, 2015 Karfe 00:01

Labarai / Sauran Duniya

Yau Ake Bukukuwan Kirsimeti A Akasarin Duniyha

Paparoma Benedict yayi addu'ar samun zaman lafiya, musamman a Gabas ta Tsakiya, a jawabinsa na jajiberen Kirsimeti.

Paparoma Benedict yana gudanar da taron ibada na jajiberen Kirsimeti a fadarsa ta Vatican, litinin 24 Disamba 2012
Paparoma Benedict yana gudanar da taron ibada na jajiberen Kirsimeti a fadarsa ta Vatican, litinin 24 Disamba 2012
Paparoma Benedict yayi addu'ar samun zaman lafiya, musamman a yankin Gabas ta Tsakiya, a lokacin da yake jagorancin taron ibada na jajiberen kirsimeti, yayin da Kiristoci a fadin duniya suke bukukuwan ranar a yau talata.

A lokacin da yake jawabi ga mabiya darikar Roman katolika da suka cika majami’ar St. Peter dake fadarsa ta Vatican cikin daren litinin, Paparoman yayi kira da a kawo karshen zub da jini a kasashen Sham da Lebanon da Iraqi da makwabtansu. Har ila yau yayi addu'ar ganin yahudawa da Falasdinawa sun zauna da juna cikin lumana.

Dubban masu ziyara daga sassa dabam-dabam na duniya sun hallara a garin Bethlehem na yankin Yammacin kogin Jordan a wurin da kiristoci suka yi imanin an haifi Yesu.

Musamman bukukuwan kirsimeti na bana sun zo cikin lokacin murna da farin ciki ga masu masaukin baki, Falasdinawa, wadanda a watan da ya shige Majalisar dinkin duniya ta amince da yankinsu a zaman ‘yantacciyar kasar Falasdinu.

A cikin hudubarsa ta jajiberen kirsimeti, babban bishop na ‘yan darikar Roman Katolika a yankin Falasdinu, Fouad Twal, yayi murnar wannan nasarar da Falasdinawa suka samu, yana kuma kira a garesu da su yi aiki tare da ‘yan Isra’ila domin kawo karshen rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa a yankin.

Sauti

 • Shirin Rana
  Minti 30

  Shirin Rana

  Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

 • Shirin Hantsi
  Minti 30

  Shirin Hantsi

  Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

 • Shirin Safe
  Minti 30

  Shirin Safe

  Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

 • Shirin Dare
  Minti 30

  Shirin Dare

  A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

 • Shirin Rana
  Minti 30

  Shirin Rana

  Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

Karin Bayani akan Shirya-shirye
Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Shirya-shirye