Lahadi, Maris 29, 2015 Karfe 14:41

Sauran Duniya

Ba Indiye Ya Fadi Yadda Aka Yi Ma Abokiyarsa Fyade

Wannan hira ta gidan telebijin na Zee TV ita ce karon farko da wannan saurayi ya fito yayai magana a kan abubuwan da suka faru ranar 16 Disamba

Wani dattijo a Indiya yana kunna kyandir a wurin tunawa da dalibar da ta mutu bayan an yi mata fyade a New Delhi, a kasar IndiyaWani dattijo a Indiya yana kunna kyandir a wurin tunawa da dalibar da ta mutu bayan an yi mata fyade a New Delhi, a kasar Indiya
x
Wani dattijo a Indiya yana kunna kyandir a wurin tunawa da dalibar da ta mutu bayan an yi mata fyade a New Delhi, a kasar Indiya
Wani dattijo a Indiya yana kunna kyandir a wurin tunawa da dalibar da ta mutu bayan an yi mata fyade a New Delhi, a kasar Indiya
Abokin wata matashiya mai shekaru 23 da haihuwa ‘yar kasar Indiya wadda ta mutu makon jiya a saboda raunukan da ta samu a lokacin da aka yi mata mummunan fyade cikin wata motar bas a New Delhi, ya fito a karon farko ya fada ma wani gidan telebijin na Indiya abubuwan da suka faru.

Wannan saurayi ya fada jiya jumma’a cewa sai da aka dauki mintoci 25 kafin wani ya tsaya ya taimake su a bayan da aka jeho su gefen hanya, tsirara, daga cikin motar.

Yace a lokacin da ‘yan sanda suka iso, sun tsaya su na ta musu da junansu a kan ko wanene yake da iko a kan wannan batun tsakaninsu.

Wannan hira da aka yi a gidan telebijin na Zee TV shi ne karon farko da wannan saurayin da ba a fadi sunansa ba, yayi magana a bainar jama’a kan harin da aka kai musu shi da wannan daliba ranar 16 ga watan Disamba.

Yace a cikin motar ‘yan sanda, ba wai a cikin motar daukar marasa lafiya ba, aka dauke shi da ita zuwa asibiti inda yace ya zauna tsirara na tsawon awoyi da yawa a kasa ba tare da an zo an duba shi ba.

Wannan daliba ta mutu ranar asabar da ta shige a wani asibitin kasar Singapore, inda aka kai ta jinya.

Hukumomin Indiya sun gurfanar da mutane 5 gaban kotu su na tuhumarsu da kisan kai, fyade, satar mutum da wasu laifuffukan. Hukumomi sun ce zasu nemi da a yanke hukumcin kisa a kansu idan an same su da laifi. Mutum na shida an ce shekarunsa bai kai 18 ba, saboda haka za a gurfanar da shi a gaban kotun yara.

Fyade da mutuwar wannan daliba sun haddasa zanga-zanga da nuna bacin rai a duk fadin kasar Indiya.
An rufe wannan dandalin
Yadda Ake Son Gani
Sharhi/Ra'ayi
     
by: abubakar suleman Daga: kaduna
06.01.2013 16:26
a gaskiya fyade babban lefine dayakamata ayi mummunan hukunci ga duk wanda akasamu ya aikatashi musamman akan yara kanana

Audio Shirin Safe :         0500 - 0530 UTC

Audio Shirin Hantsi :      0700 - 0730 UTC

Audio Shirin Rana :        1500 - 1530 UTC

Audio Shirin Dare :         2030 - 2100 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12026190548 ko kuma +12026190551.
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Sauti