Lahadi, Nuwamba 29, 2015 Karfe 18:39

Labarai / Sauran Duniya

Cutar Mura Tayi Karfi a Amurka

Cutar MuraCutar Mura
x
Cutar Mura
Cutar Mura
Cibiyar kare yaduwar cututtuka ta Amurka tace wannan shekara ce ta fi muni a yaduwar mura cikin shekaru 10 da suka wuce a nan Amurka, kuma har yanzu cutar bata kure karfinta ba.
 
An bada rahoton cewa cutar ta yadu cikin jihohi 44, kuma cibiyar tace kiyasin mutane da suke zuwa asibiti da alamun sun kamu da mura sun ninka sau biyu cikin watan da ya wuce. A wasu sassan na Amurka, asibitoci suna kin jinyar wadanda suka je da kukan mura.
 
A jiya laraba magajin garin birnin Boston ya ayyana dokar ta baci a fannin kiwon lafiya, inda  aka sami kamar karin kaso 10 cikin 100 na mutane da suka kamu d a mura idan aka kwatanta da wadanda suka yi fama da wannan larura bara a cikin wannan birnin da yake arewa maso gabashin Amurka.
 
Hukumomin kiwon lafiya na Amurka sun ce cutar ta bullo wata daya kamin lokacinda ta saba bulla cikin watan Nuwamba, kuma cutar mai karfin H3N2, tana janyo larurar mai karfi, musamman ga wadanda suka manyanta.
 
Cibiyar hana yaduwar cututtuka ta Amurkan tana bada shawarar ko mutane wadanda suke da shekarun haifuwa da  ya haura wata shida su yi allurar riga kafin kamuwa da  cutar ta mura. A shekarun baya bayan nan rigakafin yana aiki kashi 60-70 wajen hana kamuwa da cutar.

Sauti

 • Shirin Rana
  Minti 30

  Shirin Rana

  Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

 • Shirin Hantsi
  Minti 30

  Shirin Hantsi

  Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

 • Shirin Safe
  Minti 30

  Shirin Safe

  Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

 • Shirin Dare
  Minti 30

  Shirin Dare

  A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

 • Shirin Rana
  Minti 30

  Shirin Rana

  Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

Karin Bayani akan Shirya-shirye
Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Shirya-shirye