Litinin, Mayu 02, 2016 Karfe 09:13

  Labarai / Afirka

  Mali Tana Kokarin Tura Karin Sojoji Zuwa Diabaly

  Fada ya lafa a garin da ya fada hannun 'yan tawaye masu kishin Islama, amma kuma sassan na shirin sake gwabzawa kan wannan gari.

  Mayakan Islama da ke iko da arewacin Mali, na dannawa zuwa Kudu, kuma har sun kwace wani garin da shi ne mafi kusa da babban birnin kasar da ya taba shiga hannunsu, duk ko da cigaba da kai masu hari ta jiragen sama da Faransa ke yi.

  Ministan Harkokin Tsaron Faransa, Jean-Yves Le Drian, ya ce ‘yan tawayen sun kwace garin Diabaly, mai tazarar kilomita 400 a arewa da birnin Bamako, bayan wani kazamin fada da dakarun Mali.

  To amman ya ce matakan sojan da Faransa take dauka a kasar Mali su na gudana kamar yadda Shugaba Francois Hollande ya tsara.

  Wakiliyar Muryar Amurka Anne Look, tana birnin Bamako daga inda ta bayar da rahoton cewa sojojin Mali na shirin tura dakarunsu zuwa garin na Diabaly a wani yunkurin fatattakar ‘yan bindigar, wadanda aka ce su na dauke da muggan makamai.
   
  Kasar Faransa ta girke sojojinta a wannan kasar ta Yammacin Afirka ranar Jumma’a, a daidai lokacin da ‘yan tawayen da ke arewa su ka yi shirin kwace wuraren da ke karkashin ikon gwamnati.

  Jakadan Faransa a Majalisar Dinkin Duniya, Gerard Araud, ya ce Faransa ta yanke shawarar tallafa wa Mali ne saboda ta damu cewa ‘yan tawayen na iya kwace babban birnin kasar.
  An rufe wannan dandalin
  Sharhi/Ra'ayi
       
  Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

  Sauti

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shrin Safe
   Minti 30

   Shrin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye