Talata, Maris 03, 2015 Karfe 17:32

Sauran Duniya

Sanyi Ya Halaka 'Yan Gudun Hijira Su 17

Wani iyali masu gudun hijira a sansaninsu dake Kabul December 12, 2012. REUTERS/Omar SobhaWani iyali masu gudun hijira a sansaninsu dake Kabul December 12, 2012. REUTERS/Omar Sobha
x
Wani iyali masu gudun hijira a sansaninsu dake Kabul December 12, 2012. REUTERS/Omar Sobha
Wani iyali masu gudun hijira a sansaninsu dake Kabul December 12, 2012. REUTERS/Omar Sobha
Kungiyar kare ‘yancin Bil Adama ta kasa da kasa”Amnesty” ta bada rahoton cewar mutane goma sha bakwai ne suka halaka a dalilin bala’in sanyin da ake dankarawa a sansanin ‘yan gudun hijirar Afghanistan.

Don haka kungiyar ke gargadin gaggauta daukan matakan hana sake afkuwar yin watsin da aka yi da sansanonin a shekarar da ta gabata da hakan ya janyo rasa rayukan ‘yan gudun hijira dari saboda rashin kulawa.
 
Jamai’ar dake magana da yawun kungiyar ta “Amnesty” tace lallai kam da an dauki matakan da suka dace da kuwa an rage yawan asarar rayukan da ake yi ta ‘yan gudun hijira a sansaninsu saboda tsananin sanyi.

Idan za’a tuna a ziyarar aikin da ya kai Daular Kasashen Larabwa, ministan harkokin wajen Pakistan Jalil Abbas Jilani anji yana cewa za’a sako sauran fursunonin da ake tsare dasu nan bada jimawa ba. Sai dai bai yi bayanin dalla-dallar lokacin da za’a sako fursunonin ba.

Audio Shirin Safe :         0500 - 0530 UTC

Audio Shirin Hantsi :      0700 - 0730 UTC

Audio Shirin Rana :        1500 - 1530 UTC

Audio Shirin Dare :         2030 - 2100 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12026190548 ko kuma +12026190551.
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Sauti