Lahadi, Afrilu 19, 2015 Karfe 16:38

Najeriya

An Kashe Mutane 23 A Damboa Da Kano A Arewacin Najeriya

An kashe mutane biyar a Kano ran talata, yayin da aka harbe wasu 18 cikin kasuwar garin damboa dake Jihar Borno da maraicen litinin

x
Wasu mutanen da ake kyautata zaton masu kishin Islama ne sun hallaka mutane 23 a wasu hare-hare biyu dabam-dabam a yankin arewacin Najeriya.

A hari mafi muni, wasu ‘yan bindiga sun bude wuta a wata kasuwa a Jihar Borno, suka kashe mutane 18 da maraicen litinin. Wani masarauci a yankin mai suna Abba Ahmed, yace an kai harin ne a garin Damboa dake Jihar ta Borno.

Babu wani tabbas game da musabbabin kai wannan harin, amma mutanen garin na Damboa sun ce watakila an kai harin ne a kan mafarauta na garin dake sayar da irin naman nan da ake kira “Bush Meat” da turanci, wanda ya hada da naman birai, wanda musulmi a yankin ke kyama.

A wani lamarin dabam da ya faru jiya talata kuma, wasu ’yan bindiga a kan babura sun harbe suka kashe mutane 5 dake wasan dara a birnin Kano. Mutane biyu sun ji mummunan rauni a harin.

Hukumomi sun yi imanin cewa ‘ya’yan kungiyar nan ta Boko Haram ne suka kai hare-haren guda biyu.

Kungiyar ta kashe daruruwan mutane a cikin shekarar da ta shige a kyamfe da take yi na neman ganin an kafa tsarin shari’a mai tsauri a yankin arewacin Najeriya.

Hukumomi a Jihar ta Kano dai, sun hana daukar fasinja a kan babura daga ranar alhamis 24 ga watan Janairu.
An rufe wannan dandalin
Sharhi/Ra'ayi
     
Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko