Jumma’a, Mayu 06, 2016 Karfe 06:27

  Labarai / Afirka

  Bataliyar Sojan Burkina Faso Ta Isa Tsakiyar Kasar Mali

  Sojojin Faransa a cikin motocin yaki a Mali. Sojojin Faransa a cikin motocin yaki a Mali.
  x
  Sojojin Faransa a cikin motocin yaki a Mali.
  Sojojin Faransa a cikin motocin yaki a Mali.
  Wata bataliyar sojan kasar Burkina Faso ta isa tsakiyar kasar Mali, inda ta zama bataliyar sojan duk wata kasar Afrika na farko da suka isa can don bin bayan sojan Faransa dake dauki ba dadi da mayakan al-Qaida.

  A yau Alhamis ne jami’ankasar ta Mali suke bada sanarwar cewa sojoji 150 na Burkina ne suka dira a garin Markala, wani garin da tazarar km 250 ta raba shi da babban birnin kasar ta Mali, Bamako.

  Wakilin VOA Idrissa Fall dake a Bamako yanzu yace sojan na Burkina sun taru ne a wani sansanin da sojan Faransa suka taba zama lokacinda suke kokarin kama garin Derby.

  Ta wani gefen kuma, wani reshen kungiyar ‘yan kishin Islama ta Ansar Dine ta kasar Mali din yace ya balle, ya kafa tasa kungiya mai zaman kanta wacce kuma zata nemi hanyar sulhunta rikicn da ake yi da su a kasar Mali din.

  A cikin sanarwar da ta bada a yau, wannan sabuwar kungiyar dake kiran kanta Kungiyar Kishin Islama ta Azawad tace ita ma zata fito gadan-gadan ta yaki duk wata akida ta masu tsatsauran ra’ayin addini.

  Sauti

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  • Yau da Gobe
   Minti 30

   Yau da Gobe

   Yau da Gobe

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye