Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Faransa Da Na Mali Na Cigaba Da Dannawa Arewacin Mali


Sojojin Faransa na kara mai a cikin motarsu a garin Sevare dake kilomita 620 arewacin babban birnin Bamako. Junairu. 25, 2013.
Sojojin Faransa na kara mai a cikin motarsu a garin Sevare dake kilomita 620 arewacin babban birnin Bamako. Junairu. 25, 2013.
Yau jumma’a dakarun sojojin gwamnatin Mali da sojan Faransa ke baiwa rufa baya sun ci gaba da dannawa yankin arewacin kasar da yan tawaye suka mallake, yayinda aka shiga mako na uku kenan da fara fattatakar mayakan sa kai masu tsatsaurar ra'ayin Islama dake rike da arewancin kasar.

Jami’an soja sun ce hare-haren jiragen saman yakin Faransa da aka yi da dare ya kori mayakan sakan, wanda ya taimaka wa dakarun Faransa da na Mali ci gaba da kutsawa zuwa garin Gao inda yan gwagwarmayar Islamar suka fi karfi, daga inda 'yan tawayen suka arce.

Yan tawayen sun kwace yawancin arewacin Mali watanni goma da suka wuce, inda suka kafa tsatsaurar shari’ar musulunci wanda hakan ya kawo tsoron kasancewar wurin maboya ga yan ta’adda.

Bayan da suka fara dannawa kudancin kasar, faransa da tayi wa Mali mulkin mallaka a da, ta shigo cikin al’amarin bisa ga rokon da gwamnatin Mali tayi.
XS
SM
MD
LG