Asabar, Fabrairu 13, 2016 Karfe 18:06

  Labarai / Sauran Duniya

  Koriya ta Arewa Na Barazanar Daukan Mataki Akan Koriya Ta Kudu

  Motar yakin Koriya ta Arewa kennan. Motar yakin Koriya ta Arewa kennan.
  x
  Motar yakin Koriya ta Arewa kennan.
  Motar yakin Koriya ta Arewa kennan.
  Koriya ta Arewa ta yi barazanar daukar matakan mayar da murtani akan Koriya ta Kudu in har Koriya ta Kudun ta shiga cikin layin rukunin kasashen dake kokarin aiwatarda tsauraran takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ta sakawa wa Koriya ta Arewa.

  A wani bayani da aka fidda yau jumma’ daga kwamitin da arewacin kasar ta kafa akan tabbatarda zaman lafiya tsakanin arewa da kudancin kasar, kwamitin ya yi kashedin cewa sa takunkumi tamkar yin yakine da Koriya ta Arewa.

  Sanarwar kuma ta yi barazanar kawo karshen duk wata tattaunawa akan dena yin makaman nikiliya.

  Rana larabar da ta wuce, kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da harba rokar da Koriya ta Arewa ta yi a watan disambar da ta gabata, ta bayyana wannan a matsayin saba wa takunkumin da ya hana yin makami mai lizami da kuma na’urar nukiliya.

  Kan hakan ne, Koriya ta Arewa ta maido da murtani a jiya cewa zata yi gwajin makaman nukiliya zata kuma kara harba wasu rokokin.

  Sauti

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  • Yau da Gobe
   Minti 30

   Yau da Gobe

   Yau da Gobe

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye