Asabar, Nuwamba 28, 2015 Karfe 17:36

Labarai / Sauran Duniya

Dakarun Iraki Sun Bude Wa Masu Zanga-zanga Wuta

Masu zanga-zanga kennan a lokacin da suke jifar dakarun Iraki da duwatsu a garin Falluja dake Iraq, January 25, 2013.Masu zanga-zanga kennan a lokacin da suke jifar dakarun Iraki da duwatsu a garin Falluja dake Iraq, January 25, 2013.
x
Masu zanga-zanga kennan a lokacin da suke jifar dakarun Iraki da duwatsu a garin Falluja dake Iraq, January 25, 2013.
Masu zanga-zanga kennan a lokacin da suke jifar dakarun Iraki da duwatsu a garin Falluja dake Iraq, January 25, 2013.
Jami’ai sun ce dakarun Iraki sun kashe akalla 'yan zanga-zanga uku, da yawa kuma sun raunata a birnin Fallujah.

'Yan sandan sun ce 'yan zangazangar suna kan hanyar hadewa da 'yan adawar gwamnati a wani gangami da aka yi a gabashin Fallujah yayinda sojojin suka tare hanyar su.

Ganin haka ya sa yan zanga-zangar suka fara jifar dakarun da abubuwa, wanda ya sa su kuma dakarun suka bude masu wuta.

Kafofin assibiti sun tabbatarda mutuwar mutane 3.

'Yan zanga-zangar mazhabar sunni ne suka fara dunguma kan titunan yammacin lardin Anbar a watan da ya gabata a zanga-zangar da suka yi akan firayim minister Nouri al-Malik da mulkin 'yan shi’a a Iraki, wanada suka ce yana danne bukatocin ‘yan darikar su.

Sauti

 • Shirin Rana
  Minti 30

  Shirin Rana

  Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

 • Shirin Hantsi
  Minti 30

  Shirin Hantsi

  Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

 • Shirin Safe
  Minti 30

  Shirin Safe

  Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

 • Shirin Dare
  Minti 30

  Shirin Dare

  A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

 • Yau da Gobe
  Minti 30

  Yau da Gobe

  Yau da Gobe

Karin Bayani akan Shirya-shirye
Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Shirya-shirye