Asabar, Satumba 05, 2015 Karfe 00:07

Labarai / Sauran Duniya

232 Sun Mutu,100 Sun Ji Ciwo A Gidan Rawar Brazil

A cewar hukumomi da asubahin jiya lahadi gobarar ta tashi a wannan gidan rawa da ake kira Kiss

'Yan kwana-kwana na kokarin kashe gobarar da ta lankwame rayukan mutane 232 a wani gidan rawa a Santa Maria
'Yan kwana-kwana na kokarin kashe gobarar da ta lankwame rayukan mutane 232 a wani gidan rawa a Santa Maria
Halima Djimrao-Kane
Jami’an Brazil sun ce mutane 232 sun mutu, wasu fiye da 100 kuma sun ji rauni a bayan da gobara ta tashi cikin wani gidan rawa da ya cika makil da daliban jami’a a birnin Santa Maria dake kudancin kasar.

Hukumomi sun ce gobarar ta tashi da asubahin jiya lahadi a wannan gidan rawa da ake kira Kiss. Wadanda suka kubuta da rayukansu, sun ce wani daga cikin makida dake wasa a lokacin, shi ne ya kunna wani abin wasan wuta mai kama da Knockout ya cilla shi sama a dakin da suke wasa.

Da yawa daga cikin wadanda suka mutu, sun suke ne, ko kuma dai an tattaka su a lokacin da mutane ke kokawar fita daga cikin wannan gidan rawa.

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon, yace yana jimamin wannan bala’i, musamman ma ganin cewa matasa da dalibai masu yawa haka sun mutu. Ya aike da sakonsa na ta’aziyya ga iyalan mamatan.

Shugabar kasar Brazil, Dilma Roussef, ta tsinke ziyarar da take yi a kasar Chile ta koma gida a jiya lahadi a bayan wannan gobara.

Santa Maria birni ne dake da babbar jami’a da kuma mutane kimanin dubu 250. Birnin yana kuryar kudancin Brazil a kusa da inda ta yi iyaka da kasashen Argentina da Uruguay.
An rufe wannan dandalin
Yadda Ake Son Gani
Sharhi/Ra'ayi
     
by: Nura Naibi Daga: Kano Nigeria
28.01.2013 23:05
Duk wajen taruwar jamaa yana da bukatar a tanadi isassun hanyoyin fita a lokacin gaggawa, yin hakan zai iya rage asarar rayuka da dukiya

Audio Shirin Safe:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Hantsi:    1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Rana:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Dare:       1530 - 1600 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Karin Bayani akan Sauti