Juma'a, Yuli 03, 2015 Karfe 16:36

Afirka

Sojojin Faransa Da Na Mali Sun Kwace Birnin Timbuktu

Wasu Masallacen tarihi na garin Timbuktu, a Mali. (file photo)Wasu Masallacen tarihi na garin Timbuktu, a Mali. (file photo)
x
Wasu Masallacen tarihi na garin Timbuktu, a Mali. (file photo)
Wasu Masallacen tarihi na garin Timbuktu, a Mali. (file photo)
WASHINGTON, D.C -- Sojojin Faransa sun kwace ikon filin saukar jiragen sama da hanyoyin dake shiga birnin Timbuktu dake Mali, a cigaba da kokarin da suke yin a fatattakar  ‘yan yakin sa kai wadanda suka yi watani suna mamaye  arewacin Mali.
 
Jami’an Soja sunce yau litinin, sojoji laima dana kasa, tare da taimakon jiragen sama masu saukar ungulu sun kwato birnin a cikin dare.
 
Kungiyar  “UNESCO” ta Majalisar Dinkin Duniya, ta saka Timbuktu a wuraren duniya masu cike da tarihin gargajiya, saboda tsofaffin Masallacai, da wuraren gargajiya dake garin tun karni na 15. Amma kungiyar Ansar Dine na yi wa wasu wuraren kallon sabo, kuma ta lalata wasu gine-ginen gargajiya a birnin.
 
Yau Litini Magajin garin Timbuktu,  yace a lokacin da ‘yan bindigan ke gudu suna barin garin, sun cinna wuta ga wani dakin litattafai mai cike da dubunnan takardun tarihi.
 
Garin Timbuktu dai tazarar kimamin mile 300 a arewa masu yammacin birnin Gao, wajenda dakarun Faransa da na Mali suka kwace ran asabar daga hannun ‘yan bindiga ba tare da bijirewa ba.

Audio Shirin Safe:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Hantsi:    1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Rana:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Dare:       1530 - 1600 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Karin Bayani akan Sauti