Lahadi, Mayu 01, 2016 Karfe 07:04

  Labarai / Afirka

  Japan Zata Bayarda Agajin Dala Miliyan 120 Ga Sahel

  Za a yi amfani da kudin wajen kawar da tasirin masu kishin Islama a Mali, tare da maido da kwanciyar hankali a yankin Sahel na Afirka.

  Sojojin Mali su na horaswa a kusa da birnin Timbuktu a shekarar 2012, kafin yankiin ya fada hannun masu kishin Islama.Sojojin Mali su na horaswa a kusa da birnin Timbuktu a shekarar 2012, kafin yankiin ya fada hannun masu kishin Islama.
  x
  Sojojin Mali su na horaswa a kusa da birnin Timbuktu a shekarar 2012, kafin yankiin ya fada hannun masu kishin Islama.
  Sojojin Mali su na horaswa a kusa da birnin Timbuktu a shekarar 2012, kafin yankiin ya fada hannun masu kishin Islama.
  Japan zata bayar da agajin dala miliyan 120 domin kawar da tasirin masu kishin Islama a kasar Mali da kuma kokarin wanzar da kwanciyar hankali a yankin Sahel na Afirka.

  A yau talata ma'aikatar harkokin wajen Japan ta ce za a yi amfani da wani bangare na wannan kudin agajin domin karfafa rundunar AFISMA wadda kasashen Afirka suke jagoranci a kasar Mali, wadda kuma take taimakawa wajen sake kwato yankin arewacin kasar daga hannun 'yan tawaye masu kishin Islama.

  Har ila yau ta ce wannan agaji zai taimaka wajen karfafa mulki, da kyautata tsaro da rage talauci a yankin na Sahel, yanki mai yawan fama da karancin ruwan sama wanda ya kamo daga Senegal a yamma har zuwa kasar Chadi a gabas.

  Da ma dai Japan ta ba yankin agajin dala miliyan 63 a cikin shekara guda da ta shige. Har yanzu kasar ta Japan tana jimami a bayan da aka kashe 'yan kasarta su 10 a harin da wasu masu kishin Islama suka kai kan wata masana'antar gas ta kasar Aljeriya a watan nan.
  An rufe wannan dandalin
  Sharhi/Ra'ayi
       
  Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

  Sauti

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye