Lahadi, Fabrairu 14, 2016 Karfe 04:48

  Labarai / Sauran Duniya

  Faransa Ta Kamalla Aikin Kwato Mali Daga 'Yan Tawaye

  Ministan tsaron Faransa kennan, Jean-Yves Le Drian a lokacin da yake daukan hoto da sojojin Faransa a sansanin Miramas, dake kudancin Faransa. Junairu 25, 2013.Ministan tsaron Faransa kennan, Jean-Yves Le Drian a lokacin da yake daukan hoto da sojojin Faransa a sansanin Miramas, dake kudancin Faransa. Junairu 25, 2013.
  x
  Ministan tsaron Faransa kennan, Jean-Yves Le Drian a lokacin da yake daukan hoto da sojojin Faransa a sansanin Miramas, dake kudancin Faransa. Junairu 25, 2013.
  Ministan tsaron Faransa kennan, Jean-Yves Le Drian a lokacin da yake daukan hoto da sojojin Faransa a sansanin Miramas, dake kudancin Faransa. Junairu 25, 2013.
  Wani babbar kusar gwamnatin Faransa yace sun kamalla aikin kwato kasar Mali daga hannun ‘yantawaye a cikin “nasara”, amma fa yana jan kunnen cewa dole ne bangarorin kasar masu jayayya da juna su shirya a tsaianinsu – ko a koma ‘yar gidan jiya.

  A yau Alhamis ne ministan tsaron Faransa Jean Yves Le Drian yake wannan kalamin a daidai lokacinda shi kuma shugaban kasar Malin na rikon kwarya, Dioncunda Traore yake yanke kaunar duk wata tattaunawar sulhu da ‘yan kishin Islaman dake wannan tawayen, wadanda kuma suka cafke yankin arewancin kasar.

  Da yake magana da wata tashar rediyon Faransa, ministan yace sun gama cika aikin da shugaban kasarsu Francois Hollande ya basu na hana wa ‘yantawayen Mali din kutsawa zuwa cikin kudancin kasar.

  Yace yanzu Faransa tana aiki da jagabannin Mali da na kasashen Afrika don maido wa Mali cikakken ‘yancinta da martabarta, abinda yace wani abu dake tafiya a cikin hanzarin da wasu basu yi tsammani ba.

  Sauti

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye