Asabar, Nuwamba 28, 2015 Karfe 03:15

Labarai / Sauran Duniya

Iran Na Dab Da Kafa Wata Sabuwar Na'urar Sarrafa Nukiliya

Shugaban Iran kennan, Mahmoud Ahmadinejad, a lokacin da ya kai ziyara zuwa masana'antar Natanz Uranium Enrichment Facility, misalin mil 200 miles a kudancin babban birnin Tehran, Iran, Aprilu 8, 2008.Shugaban Iran kennan, Mahmoud Ahmadinejad, a lokacin da ya kai ziyara zuwa masana'antar Natanz Uranium Enrichment Facility, misalin mil 200 miles a kudancin babban birnin Tehran, Iran, Aprilu 8, 2008.
x
Shugaban Iran kennan, Mahmoud Ahmadinejad, a lokacin da ya kai ziyara zuwa masana'antar Natanz Uranium Enrichment Facility, misalin mil 200 miles a kudancin babban birnin Tehran, Iran, Aprilu 8, 2008.
Shugaban Iran kennan, Mahmoud Ahmadinejad, a lokacin da ya kai ziyara zuwa masana'antar Natanz Uranium Enrichment Facility, misalin mil 200 miles a kudancin babban birnin Tehran, Iran, Aprilu 8, 2008.
Iran na dab da saka wata sabuwar na’ura a masana’anta ta sarrafa makamashin nukiliya, wacce kuma zata bada damar sarrafa ma’adinin uranium cikin saurin da ya fi na yanzu.

Jami’an diplomasiya sun gayawa kafofin watsa labaran yammacin Turai cewa tuni Iran ta riga ta sanarda hukumar IAEA cewa tana shirin saka wannan sabuwar na’urar a ma’aikatarta ta nukiliya ta Nantaz dake tsakiyar Iran din.

Daman dai an san cewa ita wannan masana’antar ta Nantaz tana karkashin kasa ne kuma tana da dubban butacen na’urorin tace shi ma’dinin na uranium, wanda ana iya anfani da shi wajen samarda wutar lantarki, amma kuma ana iya anfani da shi wajen kera makaman kare dangi na nukiliya.

Iran dai ta sha nanatawa cewa tana son anfani da fasaharta ta nukiliya ne don inganta rayuwar al’ummarta, ba don neman tada fitina ba.

Sauti

 • Shirin Dare
  Minti 30

  Shirin Dare

  A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

 • Yau da Gobe
  Minti 30

  Yau da Gobe

  Yau da Gobe

 • Shirin Rana
  Minti 30

  Shirin Rana

  Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

 • Shirin Hantsi
  Minti 30

  Shirin Hantsi

  Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

 • Shirin Safe
  Minti 30

  Shirin Safe

  Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

Karin Bayani akan Shirya-shirye
Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Shirya-shirye