Asabar, Afrilu 30, 2016 Karfe 02:23

  Labarai / Afirka

  Kungiyar Adawar Masar Zata Ci Gaba Da Zanga-Zanga

  Masu zanga-zangan nuna kin Shugaban Masar, Mohammad Morsi a birnin Port Said Fab. 1, 2013.Masu zanga-zangan nuna kin Shugaban Masar, Mohammad Morsi a birnin Port Said Fab. 1, 2013.
  x
  Masu zanga-zangan nuna kin Shugaban Masar, Mohammad Morsi a birnin Port Said Fab. 1, 2013.
  Masu zanga-zangan nuna kin Shugaban Masar, Mohammad Morsi a birnin Port Said Fab. 1, 2013.
  Babbar kungiyar yan adawar Masar, The National Salvation Front, za ta ci gaba da da shirin yin zanga-zangar nuna adawar ta ga gwamnati a fadar shugaban kasa da ke al-Qahira yau jumma’a.

  Manyan shugabannin yan kungiyar adawa sun yi kira ga shugaba Mohammed Morsi da ya kafa hadadiyar gwamnatin kasa wadda zata basu damar shiga majalisa.

  Magoya bayan Mr. Morsi sun ki su amince da wannan rokon, akan cewar yan adawar na kokarin samun iko ne kawai wanda baza su iya samu ba ta hanyar zabe.

  Jiya alhamis yan siyasar isalama da masu sassaucin ra’ayi sun yarda su bar rikici su kuma shiga cikin tattaunawar kasa da za ayi da kudurin kawo karshen mummunan rikicin da ake yi a kasar na tsawon watanni.

  Sheik Ahmed al-Tayeb babban malamin addinin islama, shine ya shugabnci taron da aka yi a helkwatar yan sunni a alkahira, wato al-azhar.

  Ya fadawa wakilan bangarorin siyasar  kasar da ke gaba, cewa hanya daya ce kawai za a iya magance banbance-banbancen da ke tsakanin su itace ta hanyar ba da damar tattaunawa ga kowa.

  Sauti

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  • Yau da Gobe
   Minti 30

   Yau da Gobe

   Yau da Gobe

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye