Lahadi, Nuwamba 29, 2015 Karfe 20:25

Labarai / Sauran Duniya

Holder Ya Kare Manufar Yiwa Amurkawa Kisan Gilla

Atoni Janar din Amurka Eric Holder ya kare manufar gwamnatin shugaba Obama ta yin kisan gilla ga 'yan kasar Amurka da ake zargi da ta'addanci

Atoni Janar din Amurka Eric HolderAtoni Janar din Amurka Eric Holder
x
Atoni Janar din Amurka Eric Holder
Atoni Janar din Amurka Eric Holder
Halima Djimrao-Kane
Shugaban Ma’aikatar shari’ar Amurka Eric Holder ya na ci gaba da kare manufar da ake cacar baki a kai ta yin kisan gilla ga ‘yan kasar Amurka mazauna kasashen waje wadanda ake zargi da shirya ta’addanci don a kiyaye lafiyar al’ummar Amurka.

A dole aka tilastawa Holder yin bayani a jiya talata bayan da aka kwarmata wani rubutaccen bayanin ma’aikatar shari’a da ba na sirri ba wanda ya yi dalla-dalla game da manufar.

Holder ya ce majalisar dokoki ta baiwa gwamnati izinin daukan mataki akan al-Qaida da sauran kungiyoyin ta’addancin da ke fadin duniya. Ya ce kare lafiyar Amurkawa ta hanyar da ta dace da dokokin kasa ita ce babbar damuwar gwamnatin shugaba Obama.

Tun bayan kisan gillar da aka yiwa ‘yan kasar Amurka biyu a Yemen a shekarar dubu biyu da goma sha daya Fadar shugaban kasar Amurka ta White House ta kare matsayin ta game da hare-haren da jiragen saman da ake sarrafawa daga kasa ke kaiwa kan wadanda ake zargi da ta’addanci da niyar kashe su.

Jami’an gwamnati sun bayar da hujjojin kai hare-haren lokacin da su ka ce da alamar kawowa Amurka harin ta’addanci.

Amma rubutaccen bayanin da aka kwarmata ya na cewa mai yiwuwa ne shi ma dan kasa a kai mi shi harin halaka shi  idan ya na da hannu a cikin wani shirin yin ta’addanci. Haka kuma ya ce ana iya bayar da hujjar kisa in jami’an gwamnati su ka yanke cewa wanda ake zargi ba ya kamuwa.

Masanan shari’a sun ce su na da damuwar cewa yadda ake iya fassara ka’idojin manufar ta hanyoyin da dama na iya jawo kisan wani wanda bai ji bai gani ba bisa kuskure. Dan majalisar dokoki mai wakiltar jam’iyar Democrat, Jim Moran, ya ce manufar na iya zama babbar barazana ga ‘yancin walwalar Amurkawa.

Wasu ‘yan majalisar dattawan Amurka su goma sha daya sun bukaci gwamnatin shugaba Obama da ta nuna musu daukacin hujjojin shari’ar da su ka ba ta damar kai harin yiwa ‘yan kasar Amurka kisan gilla.
An rufe wannan dandalin
Sharhi/Ra'ayi
     
Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

Sauti

 • Shirin Rana
  Minti 30

  Shirin Rana

  Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

 • Shirin Hantsi
  Minti 30

  Shirin Hantsi

  Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

 • Shirin Safe
  Minti 30

  Shirin Safe

  Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

 • Shirin Dare
  Minti 30

  Shirin Dare

  A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

 • Shirin Rana
  Minti 30

  Shirin Rana

  Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

Karin Bayani akan Shirya-shirye
Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Shirya-shirye