Asabar, Mayu 23, 2015 Karfe 08:15

Afirka

Kungiyar Kasashen Musulmi Na Taron Koli A Masar

A wajen taron kolin shugabannin kasashen Musulmin sun bukaci da a dauki mataki a Mali da kuma Syria

Shugabannin kasashen Musulmin Duniya masu halartar taron koli a kasar MasarShugabannin kasashen Musulmin Duniya masu halartar taron koli a kasar Masar
x
Shugabannin kasashen Musulmin Duniya masu halartar taron koli a kasar Masar
Shugabannin kasashen Musulmin Duniya masu halartar taron koli a kasar Masar
Halima Djimrao-Kane
Shugabannin kasashen Musulmi da ke ci gaba da yin taron su na koli a Alkahira, babban birnin kasar Masar sun yi kira a kawo karshen yakin basasar kasar Syria ta hanyar tattaunawa kuma sun jinjinawa Faransa saboda gudunmowar sojojin da ta tura kasar Mali don a yaki masu tsananin kishin Islama.

Da yake jawabin bude taron a jiya laraba a gaban shugabanni hamsin da bakwai na kungiyar kasashen Musulmi, shugaban kasar Senegal Macky Sall ya bukaci sauran kasashen Musulmi su goyi bayan mulkin ‘yancin kan kasar Mali. Ya ce Kungiyar kasashen Musulmi ta duniya, ba za ta bar wasu ‘yan tsirarrun ‘yan ta’adda su aikata miyagun laifuffuka ba, su gurbata ma na addini kuma su kara bakanta Islama.

Shugaban kasar Masar Mohamed Morsi, mai masaukin bakin da ke halartar taron kolin na kwana biyu, ya sha yin tir da Allah waddai da zaman sojojin Faransa a kasar Mali a yayin da abokan kawancen shi masu kishin Islama su ka yi zanga-zanga a kofar ofishin jakadanci kasar Faransa da ke birnin Alkahira don su nuna kin yarda da sojojin ta da ta tura kasar Mali.

A cikin jawabin shi, shugaba Morsi ya yi kira ga Kungiyar kasashen Musulmi ta duniya da ta tallafawa kokarin neman hada kan da ‘yan adawar Syria ke yi kuma su jagoranci samar da canji a kasar. Ya gargadi gwamnatin da ke mulkin kasar Syria cewa ta lura da abubuwan da suka faru a tarihi kuma kar ta fifita muradun ta fiye da na ‘yan kasar.
An rufe wannan dandalin
Sharhi/Ra'ayi
     
Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

Audio Shirin Safe:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Hantsi:    1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Rana:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Dare:       1530 - 1600 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Karin Bayani akan Sauti