Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya Ta Kudu Na Zaman Ko Ta Kwana


Wani jirgin yakin Koriya ta Kudu a lokacin da yake atisayen harba roka da kan iya isa ko ina a Koriya ta Arewa. Fabrairu 14, 2013.
Wani jirgin yakin Koriya ta Kudu a lokacin da yake atisayen harba roka da kan iya isa ko ina a Koriya ta Arewa. Fabrairu 14, 2013.

A yau Alhamis Koriya ta Kudu ta nunawa duniya wani sabon rokanta da tace ingantaccen makami ne da, in an cilla shi, ba inda ba zai kai ba a cikin makwabciyar kasar da suke adawa da juna watau Koriya ta Arewa.

Koriya ta Kudu ta shiga halin zama cikin shiri da damara tun bayan gwajin da Koriya ta Arewa ta yi na wani makaminta na nukiliya da ta cilla, abinda kuma ya janyo mata la’anta daga kasashen duniya daban-daban, kuma ya kara haifarda zaman dar-dar a tsakanin Koriyoyin guda biyu.

Kakakin ma’aikatar tsaron Koriya ta Kudu, Kim Min-seok yayi bugun gaba gameda ingancin wannan sabon makamin nasu da yace an riga ma an kaddamar da shi

Koda yake ma’ai9katar tsaron ta Koriya ta Kudu bat ace ga ainihin tsawon zangon da wannan makamin zai iya ci ba, ta nuna hotunan yadda aka harba shi daga wani jirgin ruwa mai tafiya karkashin kasa da kuma yadda yake rabkawa akan abubuwan da aka harba shi a kansu.
XS
SM
MD
LG