Talata, Satumba 01, 2015 Karfe 08:55

Labarai

Faransa Ta Ce Ba Za Ta Tattauna Da 'Yan Ta'adda Ba

Faransa ta ce za ta yi iyakacin kokarin ta na ganin ta kubutar da 'yan kasar bakwai da aka sace a kasar Kamaru ana yin garkuwa da su

Ministan tsaron Faransa Jean-Yves Le Drian ya na jaddada kudirin kasar na kin tattaunawa da 'yan ta'addan kasar Kamaru baMinistan tsaron Faransa Jean-Yves Le Drian ya na jaddada kudirin kasar na kin tattaunawa da 'yan ta'addan kasar Kamaru ba
x
Ministan tsaron Faransa Jean-Yves Le Drian ya na jaddada kudirin kasar na kin tattaunawa da 'yan ta'addan kasar Kamaru ba
Ministan tsaron Faransa Jean-Yves Le Drian ya na jaddada kudirin kasar na kin tattaunawa da 'yan ta'addan kasar Kamaru ba
Halima Djimrao-Kane
Hukumomin kasar Faransa sun lashi takobin yin duk abinda yafi dacewa suyi domin kubutar da Faransawan nan bakwai da ‘yan bindiga suka sace a kasar Kamaru a makon da ya gabata.

Anji Ministan tsaron kasar Faransa Jean-Yves Le Drian, yana fadi jiya talata cewa abinda Faransa ba zata yi ba shine, tattaunawa da ‘yan ta’adda.

Ministan ya yi wannan jawabin ne bayan hotunan bidiyon da aka nuna na Faransawan bakwai ‘yan bindiga na zagaye da su, har ma daya cikin harshen larabci ya rika yin barazanar zasu kashe Faransawan muddin ba’a sako ‘yan uwansu masu kishin Islamar da ake tsare da su a Kamaru da Najeriya ba.
An rufe wannan dandalin
Sharhi/Ra'ayi
     
Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

Audio Shirin Safe:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Hantsi:    1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Rana:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Dare:       1530 - 1600 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Karin Bayani akan Sauti