Alhamis, Nuwamba 26, 2015 Karfe 00:38

Labarai / Afirka

Kungiyar Boko Haram Ta Ayyana Tsagaita Wuta.

Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau.Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau.
x
Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau.
Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau.
Aliyu Imam
Jiya litinin a Maiduguri, wani mutum wanda yake ikirarin shi kwamanda ne a kungiyar mayakan sakai da aka fi sani da Boko Haram, ya ayyana shirin tsagaita wuta na kashin kai. Babu tabbas ko kwamandan Sheikh Abu Mohammed Ibn Abdulazeez, yana magana ne a madadin dukkan kungiyar baki daya, duk da haka jami’an Najeriya suka ce zasu yi nazari kan sharuddan da kungiyar ta gindaya.
Hotunan vidiyo daga tashar talabijin ta NTA da aka dauka a bara a maidugri. Babu tabbas kan hali da mutanen nan da suke kwance suke ciki.Hotunan vidiyo daga tashar talabijin ta NTA da aka dauka a bara a maidugri. Babu tabbas kan hali da mutanen nan da suke kwance suke ciki.
x
Hotunan vidiyo daga tashar talabijin ta NTA da aka dauka a bara a maidugri. Babu tabbas kan hali da mutanen nan da suke kwance suke ciki.
Hotunan vidiyo daga tashar talabijin ta NTA da aka dauka a bara a maidugri. Babu tabbas kan hali da mutanen nan da suke kwance suke ciki.

Wannan ne karo na farko da wani mutum ya bayyana gaban ‘yan jarida yana ikirarin cewa shi dan kungiyar Boko Haram ne. Abunda aka saba gani daga 'yan kungiyar shine su kira da woyoyin da aka boye lambobinsu, ko su aike da sakon vidiyo a dandalin Youtube, ko sakon email, idan har suna da wani sako da suke so duniya ta ji.

A jawabi na minti 10 da ya gabatar, Abdulazeez yace shine na’ibin shugaban kungiyar Abubakar Sheaku, mutumin da aka hakikance shine shugaban kungiyar.

A jawabin da  ya gabatar da Hausa, Abudlazeez ya  yi kira ga ‘yan kungiyar su kwance damara, kuma su gayawa abokanansu cewa su ma su yi hakan, domin kada jami’an tsaro su kama wani “dauke da makamai ko su kashe su da sunan ‘yan kungiyar”.

Babu wanda  ya san yawan rassan kungiyar Boko Haram, kuma ko wadanne ne daga cikinsu suke mutunta umurni daga kwamanda Abdulazeez. Idan aka duna daga take takensu, wadansu suna son su kafa tsarin shari’a tsantsa, wadansu kuma suna yaki ne da jami’an tsaron Najeriya.

Kamar yadda Abdulazeez ya fada ganin sun tsagaita wutar, gwamnatin jihar Borno, jihar da a can ne tungar tawayen, ta amince  zata saki ‘yan kungiyar da ake tsare da  su. Idan kuma gwamnatin ta kasa cika abunda ya kira “alkawari”, yace rashin zaman lafiyar zai dore har abada.

Kakakin gwamnan jihar Borno, Isa Gusau bai tabbatar da cewa jami’an gwamnatin jihar sun gana da Abdulazeez ko a’a ba. Duk da haka yace Gwamna kashim Shettima, ya sha nanata kiran da  a gudanar da shawarwarin sulhu da kungiyar ta Boko Haram.

A cikin wani sakon text da ya aike cikin daren litinin, kakakin kungiyar tsaro ta musamman a jihar leftanar Sagir Musa, yace suna marhabin da shirin tsagaiata wutan, duk da haka yace ba  zasu sassauta matakan tsaro da suka dauka ba, ya kira Abdulazeez shugaban Boko Haram. Kanal Sagir bai  ce kome ba kan sharadi da kungiyar ta shimfida ba.

Watakila Za A So…

Shirin Dare

Shirin Dare

A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na yadda duniyar ta yini da rahotanni da dumi-duminsu, sannan mu kan bude muku layuka domin ku bugo ku bayyana mana ra’ayoyinku kan batutuwan da suka fi muhimmanci a wannan rana, ko kuma wadanda ke ci muku tuwo a kwarya.
Shirin Rana

Shirin Rana

Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai da dumi-duminsu daga kowace kusurwa ta duniya, musamman ma dai muhimman abubuwan da suka faru, ko suke faruwa a kusa da ku a wannan rana.
Shirin Hantsi

Shirin Hantsi

Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku da labarai da hirarraki, da sharhin jaridu kama daga Najeriya zuwa Nijar har Ghana, da kuma ra’ayoyinku.
Shrin Safe

Shrin Safe

Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da rahotanni da dumi-duminsu, sannan mu na gabatar da wasu shirye-shirye kamar Noma da Lafiya Uwar Jiki.

An rufe wannan dandalin
Yadda Ake Son Gani
Sharhi/Ra'ayi
     
by: lawan yusuf shaba Daga: uganda
20.02.2013 05:49
Ubangijin da yasa wadannan mutanen suka kwance damararsu to kuma yasa gwamnatinmu ta lura da tsaron jama,a da zaman lafia amiin

Sauti

 • Shirin Dare
  Minti 30

  Shirin Dare

  A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

 • Yau da Gobe
  Minti 30

  Yau da Gobe

  Yau da Gobe

 • Shirin Rana
  Minti 30

  Shirin Rana

  Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

 • Shirin Hantsi
  Minti 30

  Shirin Hantsi

  Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

 • Shrin Safe
  Minti 30

  Shrin Safe

  Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

Karin Bayani akan Shirya-shirye
Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Shirya-shirye