Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Honduras Ta Sha Kashi A Hannun Chile


Honduras Ta Sha Kashi A Hannun Chile
Honduras Ta Sha Kashi A Hannun Chile

Wannan shi ne karon farko cikin shekaru 48 da kasar Chile ta ke samun nasara a wata gasa ta cin kofin kwallon kafar duniya.

Chile ta doke kasar Honduras da ci daya da babu (1-0) a wasanta na farko na gasar cin kofin Kwallon Kafar Duniya ta 2010 a Afirka ta Kudu. An gwabza wannan wasa ne a garin Nelspruit.

Tun daga farkon wasan har zuwa karshensa, 'yan wasan Chile ne suka kanainaye kwallo a wannan karawa a rukunin "H" ko kuma rukuni na 8. Sau 20 'yan wasan Chile su na auna kwallo a ragar 'yan wasan Honduras, amma kwaya daya ta shige. Su kuwa 'yan Honduras sau 7 kacal suka auna kwallo a ragar Chile.

Wannan shi ne karon farko cikin shekaru 48 da kasar Chile take samun nasara a gasar Cin Kofin Kwallon Kafar Duniya.

Dan wasanta mai suna Jean Beausejour shi ne ya jefa wannan kwallo a bayan da ya doki kwallon da Mauricio Isla ya auno ta gefen gidan 'yan Honduras. Yanzu Chile ita ce take sama a wannan rukuni na "H" ko na 8.

XS
SM
MD
LG