Jumma’a, Maris 27, 2015 Karfe 20:07

Najeriya

Clinton Ta Yi Kira Ga Goodluck Jonathan Da Ya Kara Mikewa

Jami'ai suka ce Clinton ta ce a shirye Amurka ta ke ta taimaka wajen horas da jami'an tsaron kasar dake fafatawa da 'yan Boko Haram

Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton, tana ganawa da shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya a fadar shugaban a Abuja, alhamis, 9 Agusta 2012.
Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton, tana ganawa da shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya a fadar shugaban a Abuja, alhamis, 9 Agusta 2012.

Article Poll

Zaben lokutan da
Sakatariyar harkokin wajen Amurka, ta yi kira ga shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya da ya kara mikewa wajen yakar tashin hankali na tsageranci a arewaci da yankin tsakiyar kasar.

Jami’an dake tafiya tare da Clinton sun ce ta fadawa shugaba Jonathan da manyan jami’an tsaron Najeriya cewa a shirye Amurka ta ke ta taimaka wajen horas da ‘yan sanda da rundunonin yaki da ta’addanci wadanda ke fafatawa da ‘yan Boko Haram. Ana dora wa kungiyar ta Boko Haram alhakin hare-hare da dama da kuma mutuwar mutane fiye da 600 a wannan shekara kawai, a kokarinta na kafa tafarkin shari’ar Musulunci a kasar mai mutane miliyan 160.

Kungiyoyin kare hakkin bil Adama sun ce kungiyar Boko Haram ta fi yawaita hare-hare a kan jami’an tsaro da na gwamnati, da gine-ginen gwamnati da kuma majami’un Kirista a wannan kasar da kusan al’ummarta rabi Musulmi en rabi kuam Kirista.

Ya zuwa yanzu dai, gwamnatin ta Najeriya ta kasa kawo karshen wannan zub da jini.

Har ila yau, Clinton ta roki gwamnatin Najeriya da ta kara zage damtse wajen nuna gaskiya da kawar da cin hanci da rashawa a wannan kasa dake cikin wadanda suka fi kaurin suna a duk duniya wajen cin hanci da wawurar dukiyar jama’a.

Sakatariya Clinton ta kai wata gajeruwar ziyara zuwa Jamhuriyar Benin, daga nan kuma ta doshi kasar Ghana inda a yau zata halarci jana’izar marigayi shugaba John Atta Mills.
An rufe wannan dandalin
Yadda Ake Son Gani
Sharhi/Ra'ayi
     
by: nuhu usman wali dodo Daga: birnin kebbi
15.08.2012 13:43
Allah shibamuzaman lafiya ba amurukaba cinhanci da rashawa inba andenasuba bazaman lafiya


by: Nasir Amin Daga: Jigawa state
14.08.2012 12:57
agaskiya mu yan' nigeria muna bakin cikin kasancewar Amurka ta shiga tsarin mulkin kasarmu saboda ba inda suka kai taima kuma taimakon yayi amfani.


by: lawal
13.08.2012 00:21
clinton tafadi gaskiya allah yasa yakai zuciya


by: IBRAHIM AMMANI Daga: MONROVIA LIBERIA
10.08.2012 10:51
Inna fatan musulmim nigeria zasu ye amfani da wannan wata mai alfarma wajen aduoin samun zaman lafiya masaman a arewachin nigeria,amin


by: IBRAHIM AMMANI Daga: MONROVIA LIBERIA
10.08.2012 10:51
Inna fatan musulmim nigeria zasu ye amfani da wannan wata mai alfarma wajen aduoin samun zaman lafiya masaman a arewachin nigeria,amin


by: Auwal Yusuf Daga: kano
10.08.2012 08:30
VOA ku dubi girman Allah kuyi wani shiri na musamman game da su waye boko haram? Don a gaskiya mutane da dama sun dawo daga rakiyar kafafan yada labarai sabo da sun gane wannan al amari akwai hannun gwannati a ciki. Kuma don Allah ku binciko mana ina wanda aka kama za su saka bama-bamai?yaya akai dasu. Sakamakon mutane sun fara gane akwai hannun gwannatin najeriya a ciki abun ya dan lafa. Kuma ai jonathan ba sai ya kara mikewa ba, cewa zai a daina kai hari kamar yadda abin yake a yanzu. Wani abun mamaki duk wanda ake kashewa a cikin jamian tsaro musulmai ne. Idan kafafan yada labarai sun boye gaskiya to ai Allah yana ganin komai.

Audio Shirin Safe :         0500 - 0530 UTC

Audio Shirin Hantsi :      0700 - 0730 UTC

Audio Shirin Rana :        1500 - 1530 UTC

Audio Shirin Dare :         2030 - 2100 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12026190548 ko kuma +12026190551.
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Sauti