Alhamis, Mayu 05, 2016 Karfe 13:19

  Labarai / Afirka

  Cutar Kwalara Ta Barke A Yankin Darfur Na Kasar Sudan

   Wadansu yara suna jira iyayensu a dakin shan magani Wadansu yara suna jira iyayensu a dakin shan magani
  x
   Wadansu yara suna jira iyayensu a dakin shan magani
  Wadansu yara suna jira iyayensu a dakin shan magani

  Hukumar kiwon lafiya ta duniya tace tana kokarin shawo kan mummunar cutar shawara data barke a yankin Darfur na kasar Sudan.

  Hukumar ta kiwon lafiya ta fada jiya talata cewa, tana hada kai da gwamnatin Sudan wajen samun alluran riga kafin cutar har kusan miliyan biyu da  rabi domin mazauna yankin. Hukumar tace wata hadakar kasa- da kasa kan alluran rigakafi ce zata samar da alluran, wannan hadakar gamayyar kamfanonin harhada magunguna ne, wadanda suke aiki tare da Majalisar Dinkin Duniya.

  Hukumar ta bada labarin cewa cutar ta barke ne a karshen watan Satumba, tun lokacin ta sami rahoton mutane 358 sun kamu da cutar, wasu 107 kuma sun riga mu gidan gaskiya. Wadnada suke zaune a tsakiyar yankin na Darfur, sune cutar  tafi yiwa barna.
  Da yake magana da Muriyar Amurka ta woyar tarho daga Khartoum, wakilin hukumar kiwon lafiya ta duniya a Sudan Anshu Banerjee, ya bayyana cewa za a fara aikin riga kafin cikin makonni uku masu zuwa, kuma za a yi mako biyu ana gudanar da shi.

  Sauti

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  • Yau da Gobe
   Minti 30

   Yau da Gobe

   Yau da Gobe

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye